
Hukumar NDLEA tayi babban kamun Tabar Wiwi
Hukumar hana fasa kauri ta kasa reshan jihar kwara ta mikawa hukumar NDLEA Tabar wiwi ta kimanin naira miliyan N244 data kwace
Kwamandan Hukumar, hana fasa kauri na jihar Kwara, Ahmed Hussaini a ranar Talata ya mika buhu arba'in da takwas 48, na Tabar wiwi, wacce aka kwace daga hannun masu safarar miyagon kwayoyi a kan iyakokin jihar zuwa ga Hukumar yaki da sha da fataucin miyagon kwayoyi ta Kasa wato (NDLEA) a cikin jihar.
Kwamandan hukumar hana fasa kauri na Najeriya a jihar kwara, Ahmed Hussaini ne, ya bayyana haka a lokacin da yake magana da taron manema labarai, inda ya ce an kwace kayan laifinne a kananan hukumomi daban-daban kuma a lokuta daban-daban daga hannun masu safarar kayan laifin a dai-dai Bokoro a karamar hukumar Baruten dake kan titin Ilorin / Jebba a kana...