fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: Kwara

Rikicin Saka Hijabi: Bidiyon yanda matasa suka rushe Masallacin dake cikin makaranta a jihar Kwara

Rikicin Saka Hijabi: Bidiyon yanda matasa suka rushe Masallacin dake cikin makaranta a jihar Kwara

Tsaro, Uncategorized
Rikicin saka Hijabin dalibai a jihar Kwara na ci gaba da daukar wani sabon Salo inda Rahotanni na baya-bayannan na cewa wasu fusatattun matasa sun je makarantar Bishop Smith Secondary school inda suka rushe masallacin dake ciki.   Lamarin ya farune da duku-dukun yau Talata amma ba'a kai ga sanin ko su wanene suka rushe masallacin ba.   Wani Rahoton kuma yace, mahukuntar Makarantar sun tilastawa dalibai mata cire hijabansu kamin daga baya aka turasu gida.   Matasa dai sun shiga cikin makarantar suka kulle da hana dalibai da malamai shiga inda har suka hadawa kofar shiga Makarantar Shokin din wutar Lantarki, amma daga baya an yi sulhu dasu sun bude, kamar yanda Daily Post ta ruwaito.   Kalli Bidiyon a nan
Rikicin Saka Hijabi a Makarantu: Bidiyon yanda Musulmai da Kiristoci ke jifar juna da dutse a Kwara

Rikicin Saka Hijabi a Makarantu: Bidiyon yanda Musulmai da Kiristoci ke jifar juna da dutse a Kwara

Tsaro
A yaune dai Rikici kan saka Hijabi a makarantun jihar Kwara ya kazance, inda duk da Umarnin da gwamnatin jihar ta Bayar na bude makarantu 10 da aka kulle a baya kan batun, Kiristoci suka ce basu amince ba.   Kiristoci sun fito suna Zanga-zanga, yayin da Suma Musulmai suka fito suna yin tasu zanga-zangar. An kacame inda aka fara jifar juna da duwatsu har aka fasa kan wasu.    
Jami’an ‘Yan Sanda biyu sun rasa ransu Hadarin mota a Kwara

Jami’an ‘Yan Sanda biyu sun rasa ransu Hadarin mota a Kwara

Uncategorized
Jami’an ‘yan sanda biyu sun rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su bayan da motar da ke tafe da su ta afkawa wata tirelar da ke kan babbar hanyar Ilorin-Ogbomoso. Jami'an suna dawowa Ilorin ne daga Ogbomoso inda suka yi wa motar banki. "Jami'an 'yan sanda suna dawowa daga Ogbomoso inda suka yi wata motat, " in ji jami'in hulda da jama'a na' yan sanda na Kwara SP Ajayi Okasanmi. "Daya daga cikin tayoyin motar da ke rakiyar ta fashe sai ta afka cikin tirelar da aka ajiye a kan hanya." Dukkan jami’an biyu sun mutu nan take, amma wasu da hatsarin ya rutsa da su sun samu raunuka. An ajiye gawarwakinsu a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ilorin, yayin da wadanda suka jikkata aka ce suna karbar kulawar likita a asibitin. Shima kwamandan hukumar kiyaye haddura ...
Gobara ta lalata dakunan kwanan Dalubai a jihar Kwara

Gobara ta lalata dakunan kwanan Dalubai a jihar Kwara

Uncategorized
Hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ta bayyana yadda  gobara ta lalata Dakunan Dalubai Mata a makarantar Offa Grammar School, dake karamar hukumar Offa a jihar. Hakeem Adekunle, shugaban yada labarai  na hukumar shine ya shaida hakan a wata sanarwa da aka fitar a ranar Juma'a a Ilorin, ya ce wutar ta shafi Dakuna a kalla 20 yayin da Dakuna 6 suka kone kurmus. A cewarsa gobarar ta faru ne sakamakon sakaci.
An bayyana Mata a matsayin wanda ke da kaso mafi yawa da aka tabbatar dake Dauke da Cuta mai sarke Numfashi a jihar Kwara

An bayyana Mata a matsayin wanda ke da kaso mafi yawa da aka tabbatar dake Dauke da Cuta mai sarke Numfashi a jihar Kwara

Kiwon Lafiya
An bayyana Mata a matsayin wanda ke da kaso mafi yawa da aka tabbatar dake Dauke da Cuta mai sarke Numfashi a jihar Kwara A wata sanarwa da kwararriya mai bincike kan yaduwar cututtuka da shawo kan cutar a jihar Kwara Dakta Khadija Kamaludeen ta fitar ta bayyana cewa Jihar ta gwada mutane 17,581. Mai binciken ta bayyana hakan ne a wani taron yaki da cutar Korona na kullum dake gudana a jihar inda ta bayyana cewa Mata a jihar Nada kaso mafi yawa na masu Dauke da cutar inda mata keda kaso 56.6 yayin da maza keda kaso 46.4. A cewarta, Wadanda aka tantance mafiya yawan su 'yan shekaru 25 zuwa 29 ne. Ta kuma kara da cewa , A yanzu jihar nada Dakunan gwaje-gwaje har guda 12 a kananan hukumomi 16 dake jihar. Da take bayyana mutane da cutar ta kashe a jihar ta ce a kalla mutane 45 n...
Hadarin Mota yayi sanadin salwantar rayukan mutane 4 a jihar Kwara

Hadarin Mota yayi sanadin salwantar rayukan mutane 4 a jihar Kwara

Uncategorized
Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC), reshen jihar Kwara, a ranar Lahadi, ta ce mutane hudu sun mutu a wani hatsarin mota da ya afku a Ilorin, kan hanyar Ogbomoso-Ilorin. Kwamandan rundunar FRSC a jihar, Jonathan Owoade, shine ya tabbatar da hakan ga kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Ilorin. Owoade ya ce hatsarin ya afku ne sakamakon tsananin gudu da kuma tukin ganganci, inda ya kara da cewa a kalla mutane 18 ne hatsarin ya rutsa da su. A cewarsa, Hadarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi hakanan Daga cikin fasinjoji 18, mutum bakwai sun samu raunuka daban-daban, yayin da mutum hudu suka mutu.
Gwamnatin jihar Kwara ta ware Kudade domin tallafawa wadanda Ambaliya ta shafa a jihar

Gwamnatin jihar Kwara ta ware Kudade domin tallafawa wadanda Ambaliya ta shafa a jihar

Uncategorized
A ranar Laraba Gwamnatin jihar kwara zata fitar da kudade domin tallafawa mutum 2,300 da Ambaliyar ruwa ta shafa a Illorin babban birnin jihar. Gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq, a kwanakin baya ya kafa kwamiti domin kawo masa rahoton adadin barnar da Ambaliyar ruwan ta haifar, inda bayan bayyana rahoton ne gwamnan jihar ya bayar da Uamarnin fara biyan wadanda Iftila'in ya sama tallafin kudi ga kowannan su. Sanarwar ta ce za'a baiwa kowanne mutum kimanin Naira Dubu 20,50 zuwa Dubu 100 ya danganta da yawan barnar da Ambaliyar da haifar ga Mutum Inji Sanarwar.  
Gwamnatin Kwara za ta dauki malamai 4,701 aiki a jihar

Gwamnatin Kwara za ta dauki malamai 4,701 aiki a jihar

Uncategorized
Gwamnatin jihar kwara ta shelanta shirinta na daukar sabbin malamai har kimanin 4,701 a jihar. A cewar, Gwamnatin jihar zata Dauki malaman ne amma wadanda suka samu  shaidar Karatun NCE kuma wadanda suka ci darasi 5 wanda ya hada da Turanci da lissafi ka dai. Hakanan Gwamnatin jihar ta fitar da Addireshan da za'a bi domin neman shiga shirin (https//subeb.kw.gov.ng). wanda zai fara a ranar 3 ga watan Janairu ya kuma kare 16 ga watan.  
Adadin mutane 253 suka rasa rayukansu sanadiyyar hadura a jihar Kwara

Adadin mutane 253 suka rasa rayukansu sanadiyyar hadura a jihar Kwara

Uncategorized
Hukumar kiyaye hadura FRSC reshan jihar Kwara ta bayyana cewa, kimanin mutane 253 a jihar suka rasa ransu a sanadin haduran mota da suka afku a fadin jihar a taskanin watan Janairu zuwa watan Nuwamban shekarar 2020. Kwamadan hukumar na jihar Jonathan Owoade shine ya shaida hakan ga manema labarai, inda ya bayyana cewa, an samu adadin hadura 321 a jihar wanda kuma ya rutsa da adadin mutane 2,399. Hakanan shugaban hukumar ya ce, a kalla mutane 1,103 ne suka samu raunuka yayin da adadin mutum 253 suka rasa ransu.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya kaddamar da rabon gidajan Sauro A jihar

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya kaddamar da rabon gidajan Sauro A jihar

Kiwon Lafiya
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na yaki da cutar zazzabin cizon sauro, wanda masana kiwon lafiya suka bayyana cewa, cutar na haddasa yawan mace mace da dama a yankunan Afurka. Gwamanan ya sha al'washin rarraba gidajan sauro gida-gida a jihar. Da yake jawabi a bikin kaddamar da rabon gidajan sauran, gwamanan ya bayyana cewa, kaso 50 na rahotan da hukumomin lafiya a jihar su ka fitar daga Asbitocin gwamnatin jihar na da alaka da zazzabin cizon sauro. Gwamanan wanda ya ce sama da 'yan jihar mutum 5,000 ne, a ka basu horo domin aiwatar da rabon gidajan sauran a kananan hukumomi 16 dake jihar. An dai shirya rabon gidajan sauran kimanin Miliyan biyu da dubu dari a jihar domin taimaka al'ummar jihar wajan yin riga kafin cutar.