fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Kwarankwatsa

Kwarankwatsa ta yi ajalin mutane 20

Kwarankwatsa ta yi ajalin mutane 20

Uncategorized
Mutane 20 sun rasa rayukansu sakamakon fadowar kwarankwatsa a yankin Kintele na wajen garin Brazaville Babban Birnin Kasar Jamhuriyar Kongo.     Shugabar gundumar Kintele Stella Mensah Sassou Nguesso ta bayyana cewar bayan kwarankwatsar ta fado kan wayoyin raba lantarki masu hatsari ne sai wuta ta kama wadda ta yi ajalin mutane 20.     Nguesso ta kuma ce wasu mutanen da dama sun jikkata inda tuni aka kai su asibiti.     Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewar wata wuta mai karfi da ta kama tare da fadowa kan tituna ne ta yi ajalin mutanen.     A Jamhuriyar Kongo da ke yankin da ake da zafin yanayi, kwarankwatsa na yawan fadowa idan ana tafka ruwan sama wanda hakan ke kashe mutane da dama.