fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: Kwaroron Roba

Mahukunta sun kama wasu dake wanke Kwaroron roban da aka yi amfani dashi dan sake sayarwa mutane

Mahukunta sun kama wasu dake wanke Kwaroron roban da aka yi amfani dashi dan sake sayarwa mutane

Uncategorized
Mahukunta a kasar Vietnam sun kama tulin kwaroron roba wanda aka yi amfani dashi da yawansa ya kai 324,000 a wani gidan da ake wankeshi dan sake sayarwa da mutane.   Ma'aikata a gidan da aka kama sun bayyana cewa suna wanke kwaroron robar su busar dashi dan sake sayarwa.   Me gidan da ake wannan aiki, Pham Thi Thanh Ngoc 'yar kimanin shekaru 33 ta bayyana cewa wani mutum ne ke kawo mata Kwaroron robar da aka yi amfani dashi.   Rahotanni sun bayyana cewa, ana kai kwaroron robar otal otal da shaguna inda an samu wasu har an shirya za'a fitar dasu, kamar yanda VN ya ruwaito.
Nan gaba kadan za’a samu karancin kwaroron Roba>>Inji Kamfanin dake yinsa

Nan gaba kadan za’a samu karancin kwaroron Roba>>Inji Kamfanin dake yinsa

Kiwon Lafiya
Babban kamfanin yin kwaroron roba na Duniya, Karex Bhd ya bayyana cewa nan gaba kadan za'a iya samun karancin kwaroron robar.   Shugaban kamfanin, Goh Miah Kiat ne ya bayyanawa jaridar Bloomberg haka inda yace yanzu yawan kwaroron robar da suke yi ya ragu da kaso 50 cikin 100 inda ya kara da cewa kuma wanda suke dashi a ajiye zai kai nan da zuwa watanni 2 ne kachal.   Yace Sanadin zaman gida da gwamnatocin kasashen Duniya suka saka ne yasa ma'aikatansu basa iya aiki saidai rabi da rabi. Saidai yace duk da haka suna biyan ma'aikatansu cikakken Albashi.   Ya kara da cewa bukatar kwaroron Roba ya karu sosai inda ya nunka saboda mutane da yawa yanzu basa son haihuwa saboda basu san abinda zai faru ba nan gaba.   Ya kara da cewa basu taba samun tangar...