fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Kwayoyi

Hotuna:Gwamna Zulum ya jagoranci kona tulin miyagun kwayoyin da NDLEA ta kona a Borno

Hotuna:Gwamna Zulum ya jagoranci kona tulin miyagun kwayoyin da NDLEA ta kona a Borno

Uncategorized
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya jagoranci kona tulin miyagun kwayoyi da suka kai tan 20 da hukumar NDLEA ta kona a Borno.   Lamarin ya farune a jiya, Juma'a a hanyar Maiduguri zuwa Gamboru, hmtaron ya samu halartar Shehun Borno wanda ya tura wakilci da kuma kwamandan sojoji da shugaban NDLEA, Kanal Mustapha Abdallah me riyata. Gwamnan a yayin bikin ya bayyana damuwa kan yanda ta'ammuli da miyagun kwayoyi ka iya saka rayuwar matasa cikin hadari. Ya kuma bada umarnin gyaran rukunin gidajen hukumar dake Borno a matsayin tallafi daga jihar.
NDLEA ta kame mutane 327 da kilo 660.15 na miyagun kwayoyi a jihar Jigawa

NDLEA ta kame mutane 327 da kilo 660.15 na miyagun kwayoyi a jihar Jigawa

Uncategorized
Hukumar hana sha da fataucin kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta ce ta kama mutane 327 da ake zargi da mallakar kwayoyi masu nauyin kilo 660.15 a cikin jihar Jigawa. Kakakin hukumar na jihar Jigawa, Garba Abubakar Alhaji ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya bayar ga manema labarai a Dutse don tunawa da ranar yaki da shan Magunguna ta duniya 2020 tare da taken "Ingantaccen Ilimi don Kyautata Kulawa". Ya yi bayanin cewa kayan da aka kama sun hada da wiwi, kwayar Tramadol, Rohypnol, Exol5, Vitamin 5, Diazepam, maganin tari da codeine, da kuma wasu magungunan. Garba ya ce kararraki 81 an gurfanar dasu a gaban Kotun kolin Tarayya da ke Dutse, an yanke ma mutum 25 hukunci yayin da ake tsare da mutane 56. Ya kara da cewa an ba wasu shawarwari, yayin da mutane biyu ke cikin kulawa...