
Da yiyuwa Mbappe ya ba zai buga wasan PSG da Real madrid ba a gasar zakarun nahiyar turai
Tauraron dan wasan gaba na kungiyar Paris Saint Germain, Kylin Mbappe ya samu rauni a kafar sa ranar litinin ana tsaka da atisayi.
Kuma hakan ka iya sa dan wasa ya rasa wasan PSG da Madrid na biyu a zagaye na kungiyoyi 16 na gasar zakarun nahiyar turai.
Kylian Mbappe ne dan wasan daya ciwa PSG kwallo guda a wasan farko da suka buga da Madrid a gasar ranar 15 ga watan febrairu.