fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: La liga

Gara na lashe kofin La Liga akan na lashe kyautar Pichichi sau takwas>>Messi

Gara na lashe kofin La Liga akan na lashe kyautar Pichichi sau takwas>>Messi

Wasanni
A ranar litinin Messi aka baiwa Lionel Messi kyautar Pichichi karo na bakwai wanda hakan yasa yanzu ya wuce Telmo Zarra ya zamo dan wasan da yafi lashe kyautar a tarihi, amma duk da hakan dan wasa ya bayyana cewa yafi fifita lashe kofin La Liga akan kyautar. Pichichi kyauta ce wadda aka baiwa dan wasan daya fi zira kwallaye masu yawa a  kowace kaka ta gasar La Liga, kuma Messi da Ronaldo sun dauki tsawon shekaru suna fafataea wurin lashe kyautar kafin Ronaldo ya koma Serie A shekara ta 2018. Bayan Messi ya lashe kyautar, ya tattauna da Marca kuma ya bayyana masu cewa bai san ko zai lashe kyautar karo na 8 ba, sannan shi baya tunani akan hakan saboda kyautar bata dame shi ba, hasalima yafi fifita lashe kofin gasar La Liga akan kyautar Pichichi. A karshe Messi ya kara da cewa ...
A karin Farko, Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona:Bidiyon Kuskuren da Golan Barca ya tafka da ya jawo aka ci su kwallon

A karin Farko, Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona:Bidiyon Kuskuren da Golan Barca ya tafka da ya jawo aka ci su kwallon

Wasanni
Atletico Madrid ta yi nasara akan Barcelona a wasan da suka buga jiya da ci 1 me ban haushi. Yannick Carrasco ne ya ciwa Atletico Madrid kwallonta bayan dawowa daga hutu Rabin Lokaci.   Wannan nasara ta Atletico Madrid akan Barcelona itace irin ta ta farko cikin kusan sama da shekaru 10 da suka gabata.   Nasarar ta baiwa Atletico Madrid damar komawa ta 2 a saman teburin gasar La Liga da maki 20, daidai dana Real Sociedad dake saman Teburin.   Golan Barcelona, Marc Andre ter stergen ne ta tafka gagarumin kuskuren da yasa aka ci kungiyar kwallo, inda ya fito cikin fili ya bar ragarsa.   Sau 5 kenan golan yana kuskuren da ke kaiwa ana cin kungiyar tasa tun daga watan Afrilun 2019 da ya gabata zuwa yanzu. A gasar La Liga,  babu golan da ya kaishi aik...
Na gaji da dora min matsalolin kungiyar Barcelona da ake yi>>Messi

Na gaji da dora min matsalolin kungiyar Barcelona da ake yi>>Messi

Wasanni
Kaftin din Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewa ya gaji da dora mai matsalolin kungiyar da ake yi, kuma hakan ya biyo baya ne bayan tsohon wakilin Griezmann, Eric Olhat ya bayyana cewa Messi ne yake juya kungiyar ta Barcelona. Messi ya bayyanawa manema labarai hakan ne yayin daya dira a tashar jirgin El Prait gami da komawa Barcelona da zai yi bayan ya gama bugawa kasar shi ta Argentina wasanni. A koda yaushe Antoine Griezmann yana fadin cewa babu wata matsala a dangantakar shi da Messi amma wannan furucin da kaftin yayi babu abinda zai sa sai dai a cigaba da rade raden cewa har yanzu yana kan bakar shi na barin kungiyar Barcelona idan kwantirakin shi ya kare. “I’m tired of always being everyone’s problem at the club,” the 33-year-old announced. “I get...
Atletico Madrid ta samu nasara a wasannin La Liga guda 23 a jere karo na farko a tarihi bayan ta lallasa Cadiz 4-0

Atletico Madrid ta samu nasara a wasannin La Liga guda 23 a jere karo na farko a tarihi bayan ta lallasa Cadiz 4-0

Wasanni
Tauraron dan wasan Atletico Madrid Jao Felix yayi nasarar cin kwallaye guda biyu yayin da Marcos Llorente da Luiz Suarez suka kara ciwa Diego Simone kwallaye biyu a wasan da suka lallasa Cadiz 4-0 jiya a gasar La Liga. Nasarar da Atletico Madrid suka yi tasa yanzu sun buga wasannin La Liga guda 23 a jere ba tare da cisu a wasan ba karo na farko a tarihin su, kuma yanzu sun komn saman teburin gasar da maki 17. Atletico Madrid tayi nasarar cin wasannin ta guda hudu a cikin wasanni biyar da suk gabata tun bayan da kungiyar Bayern Munich ta lallasata 4-0 a gasar zakarun nahiyar turai.
Luiz Suarez na shirin komawa kungiyar hamayyar Barcelona ta Atletico Madrid

Luiz Suarez na shirin komawa kungiyar hamayyar Barcelona ta Atletico Madrid

Uncategorized, Wasanni
Rahotanni da dama sun bayyana cewa Luiz Suarez yana shirin komawa Juventus daga Barcelon yayin da har ya amince da kwantirakin shekaru uku, amma kuma yanzu an samu labari cewa dan wasan ba shi da ra'ayin barin kasar Sifaniya.   Deportes Cuatro ne suka bayyana cewa Suarez ya dakatar da maganar komawar shi Juventus bayan ya samu labari cewa Diego Simone yana neman shi domin ya bugawa Atletico Madrid wasa, kuma ya maye masu gurbin Alvaro Morata da Diego Costa wanda ake sa ran zasu bar kungiyar bada dadewa ba. Suarez yana so ya cigaba da zama a kasar Sifaniya saboda iyalan shi suna son garin kuma komawa Atletico zai taimakama mai duk da dai TV3 sun bayyana cewa ian har bai komawa Juve ba ko Madrid to zai cigba da wasa a Barcelona saboda Koman ya canja ra'ayin shi na siyar da da...
Ba fada muke yi da Lionel Messi ba>>Shugaban La Liga

Ba fada muke yi da Lionel Messi ba>>Shugaban La Liga

Uncategorized
Kungiyar Barcelona bata yi kokari ba a kakar wasan data gabata kuma bata lashe kofi ba wanda hakan yasa tauraron dan wasan ta Messi yayi yunkurin barin kungiyar kyauta amma suka hana shi. Messi ya fadi cewa bashi da wani zabi sai dai ya cigaba da wasa a kungiyar saboda La Liga ta bayyana cewa ba zai bar Barcelona ba sai a farashin yuro miliyan 700 wanda kuma babu kungiyar da zata biya wa'yan nan kudaden musamman a cikin wannan yanayin na annobar korona. Shugaban La Liga Javier Tebas yanzu ya kare hukumar gasar akan maganar data yi na farashin Messi, yayin da yake cewa su ba fada suke yi da Messi ba kuma ba zasu taba yin fada da shi ba saboda ya kasance tarihin gasar su na kuan shekaru 20 kuma suna son shi sosai. Shugaban ya kara da cewa a matsayin su na hukumar gasa ya kamata ...
Sergio Ramos ya bugawa Real Madrid wasanni 450

Sergio Ramos ya bugawa Real Madrid wasanni 450

Wasanni
Tauraron dan kwallon kungiyar Real Madrid,  Sergio Ramos ya bugawa kungiyar tasa wasannin La liga 450.   Ramos ya bugawa na 450 ne a jiya a karawarsu da Getafe wanda shine ma yaciwa kungiyar kwallo 1 tilo ta hanyar bugun daga kai sai gola wadda ta bata damar ci gaba da rike matsayinta na 1 a saman teburin La liga da tazarar maki 4 tsakninta da Barcelona. https://www.instagram.com/p/CCKIhCao-Lc/?igshid=1poq0g88d7ycl Kungiyar ta yi murnar wannan nasara da Ramos ya samu inda ta saka hotonshi shinda shugaban Kungiyar, Florentino Perez suna rike da riga me dauke da 450.