fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Labarai

Ina cikin matsi kan fitar da sunayen ministoci amma mutanen dana sani kadai zan nada>>Shugaba Buhari

Uncategorized
Labarai na yau na nuni da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana akan fitar da sunayen ministocinshi inda ya bayyana cewa an matsamai akan ganin ya fitar da sunayen amma ba zai yadda wani ya takuramai yayi hakan ba. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Shugaban yayi wannan maganane a daren jiya, Alhamis yayin liyafar cin abincin dare da ya shiryawa shuwagabannin majalisar tarayya a fadarshi dake Abuja,kamar yanda labarai daga sanarwar me magana da yawunshi, Femi Adesina ya fitar. Da yake magana a wajan taron, shugaban yace,na san da yawanku nan kuna so kuga sunayen ministoci saboda ku tafi hutu hankulanku kwance, ina cikin matsi akan fitar da sunayen ministocin amma bazan yadda wannan yasa in yi gaggawar yin hakan ba. Labarai sun ci gaba hakamar...

Sunayen Sabbin ministocin shugaba Buhari

Uncategorized
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labarai na yau dake fitowa daga jaridar The nation na cewa 12 zuwa 15 cikin tsaffin ministocin shugaban kasa, Muhammadu Buhari zasu sake samun mukamin nasu. Sunayen ministocin kamar yanda labarai suka bayyana tuni har sun kai ga hannun kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal, saidai babu tabbacin hakan. Dokar kasa dai ta baiwa shugaban kasa dama ya nada ministoci 36 zuwa 42. Kuma labarai na nuna cewa, shugaban na son ci gaba da tafiya da wasu daga cikin ministocin saboda bajintar da suka nuna. Labarai dai daga The Nation din sun ci gaba da cewa, ministocin da ake sa ran zasu sake komawq kan mukamansu sune, ministan shari'a, Abubakar Malami ( SAN), ministan Ilimi, Adamu Adamu, ministan sufurin jiragen sama, Hadi ...

Muna jiran sunayen ministoci: Majalisar tarayya ta gayawa bangaren zartaswa

Uncategorized
Majalisar dattijai a yau, Talata ta bayyanawa fadar shugaban kasa cewa tana jiran jadawalin sunayen mutanen da shugaban kasar ke son baiwa mukaman ministoci a duk sanda aka kammalasu dan su kuma su tantance su. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Hakan na cikin Rahoton labaran yau da jaridar The Nation ta wallafa inda aka jiwo cewa majalisar ta kuma ce jiran zuwan sunayen ministocin ba zai hanata tafiya hutun sararawa ba idan lokacin hakan yayi. A karshen watannan da muke ciki na Yuli ne ake sa ran 'yan majalisar zasu tafi hutun sararawa. Shugaban kwamitin dake kula da watsa labarai da hulda da jama'a na majalisar, Sanata Adedayo Adeyeye aya bayyana cewa basu da hurumin da zasu tursasa wa bangaren zartaswa ko kuma tambayar su ko kuma su sau akan shi...

Shugaban majalisa yaje duba dansandan da ‘yan shi’a suka jiwa rauni

Uncategorized
Zuwan mabiyan shi'a majalisar tarayya a yau, Talata na daya daga cikin labarin yau da ya fi daukar hankula saboda zanga-zangar ta rikide zuwa tarzoma bayan da 'yan shi'ar suka kutsa kai cikin majalisar suka kuma lalata ababen hawa da gilasan tagunan ginin majalisar hadi da jiwa 'yansanda 4 rauni wanda har daya daga cikinsu ya mutu. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); A rahoton da Jaridar The Nation ta wallafa, ta bayyana cewa daya daga cikin 'yansandan dake cikin jini da kuma harbin bindiga a jikinshi ya bayyana cewa bindigar da aka harbeshi da ita ba ta gargajiya bace, kirar AK 47 ce. Wannan hoton na sama kakakin majalisar Dattijanne, Femi Gbajabiamila da mukarrabanshi a yayin da ya kaiwa daya daga cikin 'yansandan ziyara a asibiti dan dubashi. Rahotann...

Duba yanda jama’a suka taru a wajan bude ofishin Kwankwasiyya a jihar Nasarawa

Uncategorized
Da alama canja shekar da jagoran kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi daga   APC zuwa PDP bata sa wasu masoyanshi juya mai bayaba, wadanan hotunan irin yanda jama'a suka fitone da jajayen huluna a jihar Nasarawa wajan kaddamar da ofishin Kwankwasiyyar. Sanata Kwankwaso dai na daya daga cikin wadanda ake sa ran zasu fito neman takarar shugabancin kasarnan a zaben shekarar 2019.

Da sanin Buhari aka kori Lawal Daura>>Fadar shugaban Najeriya

Uncategorized
Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya ce kan Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a hade yake. Femi Adesina ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake gana wa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta kasar wanda aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja ranar Laraba. Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya shugabanci taron. Shugaba Buhari ya fara hutun kwana 10 ne a birnin Landan ranar Juma'a. Bayan an kammala taron, manema labarai sun tambayi Mista Adesina ya fayyace musu ko Shugaba Buhari na da masaniya a kan korar da mukaddashin shugaban kasar ya yi wa shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Lawal Daura. Mista Osinbajo ya sallami Lawal Daura ne bayan da wadansu jami'an hukumar DSS wadanda s...

Karanta labarin yanda jami’an DSS sukayi farin ciki da korar da akawa Lawal Daura

Uncategorized
Jami’an Hukumar tsaro ta DSS masu fararen kaya sun yi farin ciki da jin labarin cewa Mukaddashin Shugaban kasa watau Farfesa Yemi Osinbajo ya sallami Lawal Daura daga aiki jiya. Majiyar mu ta bayyana mana cewa an barke da murna da shewa a sa’ilin da labari ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo wanda shi ke rike da kasar na rikon kwarya ya kori Shugaban Hukumar DSS Lawal Daura daga ofis. Har a Hedikwatar DSS wanda ake kira Yello House, Ma’aikata sun yi farin cikin jin cewa an sallami Shugaban na su daga aiki. A 2015 ne Shugaba Buhari ya dawo da Lawal Daura ofis ya rike DSS bayan an yi masa ritaya a baya. Jami’an tsaron da aka aika su tare Majalisar kasar jiya ma sun ji dadin jin labarin cewa Lawal Daura ya bar ofis. An dai soki abin ya auku jiya a Majalisar kasar wanda yayi ...

BUHARI BAI TSINANA MANA KOMAI BA>>SARKIN DAURA

Uncategorized
Mai martaba sarkin Daura, Dr. Umar Faruq Umar, a ranan Litinin ya ce jama'arsa da mutanen Daura na cikin halin kunci duk da cewa dansu, shugaba Muhammadu Buhari, ne shugaban kasa. Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawo hankalin ministocin da suka amfana da matsayin da shugaba Muhammadu Buhari ya basu na su kawo agaji masarautar ta ayyuka da noma. Sarkin ya yi jawabi ne lokacin da ya karbi bakuncin ministan noma da raya karaka, Dakta Audu Ogbeh, wanda ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin a garin Daura.

‘Mace za ta iya marin mijinta don Buhari’

Uncategorized
Shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina, Alhaji Shittu Sh'aibu Shittu, ya ce taba Buhari a siyasar jihar wani abu ne mai wuya, inda ya ce matar wanda ya soki Buhari za ta iya marinsa. Alhaji Shittu ya yi wannan kalaman ne a lokacin da yake mayar da martani game da zargin da bangaren 'yan APC akida ke yi na cewa gwmanatin APC mai mulki a jihar ta saki hanyar cika alkawuran da jam'iyyar ta dauka wa al'ummar jihar. A hirarsa da Ibrahim Isa, shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina ya ce: "Wasu mutane ne da suka sha kayi a zabe. Suna ganin suna da damar da ya kamata a ce sun samu mukamai a gwamnatin tarayya, kuma Allah bai sa an samu ba, kuma ba su mayar da al'amarinsu ga Allah ba." Da aka tambayi dan siyasar cewa ko akwai wani shiri da gwmamnatin ke yi na janyo mutanen jiki. Sai ya ce...

Illar da ke tattare da tsoho ya auri karamar yarinya

Uncategorized
Jagorar mata a rundunar Hukumar Hisbah ta jihar Kano, Najeriya, Dr. Zahra'u Muhammad Umar, ta ce akwai matsala babba dangane da aurar da kananan yara mata ga tsofaffi. Ta ce duk da cewa batun tsoho ya auri karamar yarinya wani abu ne da tasha faman tattaunawa a kai, har ma kuma ta fafata da malaman addini masu kare irin wannan muradi. Kusan za a iya cewa auren karamar yarinya ga tsaffi wani batu ne da ba kasafai ake tattauna shi ba sakamakon rashin haramcinsa a addini da al'ada. To sai dai Dr Zahra'u ta ce duk da cewa addini bai haramta irin wannan aure ba amma zamani da irin illolin da ke tattare da wannan aure ka iya sa a sanya masa ayar tambaya. bbchausa.