fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Tag: labarain wasanni

Barcelona sun ba Man U ‘yan wasa biyu da miliyan 45 ta basu Pogba amma tace bata yadda ba

Uncategorized
Maganar siyen tauraron dan kwallon kafar Manchester United, Paul Pogba da Barcelona ke son yi na kara yin karfi kuma ta nuna da gaske take, domin kuwa zuwa yanzu Barca ta bayar da 'yan wasanta guda biyu da kudi Yuro miliyan 45 akan Pogban amma Man U tace bata yadda ba. A bara, lokacin da aka bude kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa, Manchester United ta nuna son sayen Andre Gomes, a bana kuma ta nuna tana son sayen Yerry Mina wanda duka 'yan kwallon Barca ne, shine Barca tayi amfani da wannan dama ta baiwa Man U din 'yan wasan guda biyu da kudi Yuro miliyan 45 dan a bata Pogba amma Man U tace, inaaa, bata yadda da wannan zancenba, ko kusa ba zata sayar da Pogba a haka ba. Masoyan kungiyar Man U suma ba'a barsu a baya ba wajan magana akan wannan ciniki inda da dama suka...

Burnley ta sayi golan Manchester City a kan fam miliyan 3.5

Uncategorized
Burnley ta sayi golan Manchester City Joe Hart a kwantaragin shekara biyu a kan fam miliyan 3.5. Shugaban kungiyar Sean Dyche ya sayi golan ne tare da saurarn gololi biyu wato Nick Pope da Tom Heaton. Hart, wanda ya yi wa kasar Ingila wasanni 75, ya kuma yi wa City wasanni 350, inda suka lashe kofin Firimiya biyu da kuma Kofin FA daya. Golan ya fara nuna sha'awar barin City ne tun bayan da Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya rika ajiye shi a benci. Sau daya Hart ya kama wa City gola tun bayan da Guardiola ya zama kocin kungiyar a shekarar 2016. Ya kuma kwashe kaka biyu a matsayin aro a kungiyar Torino da kuma West Ham. Hakazalika kasar Ingila ba ta je da shi gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha a shekarar 2018. BBChausa.

‘Yar kauye ta zo birni: Wani ya gayawa Nafisa Abdullahi bayan data wallafa wadannan hotunan nata daga kasar Ingila

Uncategorized
Tauraruwar fina-finan Hausa Nafisa Abdullahi kenan a kusa da tambarin kulub din wasan kwallon kafa na Chelsea, jiya ne dai Ali Nuhu da Ita da Ramadan Booth sukaje kallon wasan da aka buga tsakanin Chelsea din da Manchester United, wadannan kari ne akan hotunan jiyan. Jaruman na Fina-finan Hausan dai sunje kasar Ingilane inda aka karramasu da wasu lambobin yabo wanda jaridar African Voice ta basu Ali Nuhu ne ya musu jagora zuwa gurin karbar wadannan kyautukan da aka basu. Bayan da aka gama bikin karramasu dinne sai suka fantsama gari dan kashe kwarkwatar idanunusu. Bayan data wallafa wadannan hotunan nata ne a dandalinta na sada zumunta da muhawara sai wani ya mata tsiya da cewa, "'yar kauye anzo birni" Dukkansu muna musu fatan Alheri da kuma Allah yasa su gama abinda su...

Watakila Neymar zai maye gurbin Ronaldo a Madrid: Baban Neymar din ya gana da me kulub din Real Madrid akan wannan batun

Uncategorized
Rahotanni daga jaridar The Sun ta kasar Ingila sun bayyana cewa mahaifin dan wasan kwallon kafa da yafi kowane tsada a Duniya Neymar da yanzu haka yake bugawa kungiyar kwallon kafa ta PSG wasa, ya gana da me kulub din kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez akan yiyuwar maye gurbin Cristiano Ronaldo da danshi Neymar. A shekarar 2021 ne idan Allah ya kaimu kwantirakin Cristiano Ronaldo da ya sawa hannu na bugawa Real Madrid din wasa zai kare, shine baban Neymar din yake so ya kama kafa dan ganin danshi ya maye gurbin Ronaldon. Shi dai Neymar wanda ya koma PSG daga Barcelona akan makudan kudi da suka kai sama da fam miliyan dari biyu wanda hakan yasa ya zama dan kwallo mafi tsada a Duniya, an ruwaito wasu tsegumi dake cewa dan wasan baya jin dadin zama a PSG din, amma irin yanda ...