fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Labaran Duniya

Da Duminsa:Sheikh Abduljabbar Kabara ya tuba

Da Duminsa:Sheikh Abduljabbar Kabara ya tuba

Uncategorized
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya nemi afuwar waɗanda suka "fahimci cewa shi ne ya ƙiƙiiri kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW" da ake zarginsa da yi. Cikin wani saƙon sauti da ya fitar a ranar Lahadi, an ji malamin na cewa "idan har waɗannan kalamai daga ni suke, ƙirƙirarsu na yi, babu su a litattafai to lallai ya isa babban laifi da ya wajaba a gare ni na gaggauta tuba". Ya ƙara da cewa: "Amma idan ba daga ni ba ne, daga cikin waɗancan litattafai ne, to wannan kuma ya zama wani abu daban. Sai mu yi roƙon Allah ya haska wa al'umma su tashi tsaye mu taimaki addininmu, mu fitar da hadisan ƙarya daga ciki domin gudun kar a rusa mana addinin da su." Cikin wata hira da BBC, Abduljabbar ya jaddada cewa yana neman afuwar waɗanda suke ganin kalaman da ake cewa y...