
A kiyaye: Wadannan Abubuwan basa maganin Coronavirus/COVID-19
Hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta gargadi 'yan Najeriya dasu kiyaye wani sako dake yawo a shafukan sada zunta kan wasu abubuwa da aka ce suna warkar da cutar Coronavirus/COVID-19.
Hukumar tace, Lemun tsami, Manja, citta, tafarnuwa, kuskure baki da ruwan gishiri,sha ko wanke jiki da sinadarin Dettol duk basa maganin cutar Coronavirus.
https://twitter.com/NCDCgov/status/1244898669293457408?s=19
Akan samu labaran karya na yawo a shafukan sada zumunta kan cutar ta Coronavirus/COVID-19.