Wata sananniyar me gabatarda shirye-shirye, Rachel ta ziyarci IBB: Sunsha hannu har sau biyu: Ta yabeshi sosai
Wata sananniya me gabatar da shirye-shirye a kafafen watsa labari kuma 'yar rasjin kare hakkin bil'adama me suna Rachel Bakam ta kaiwa tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida(IBB) ziyara a gidanshi dake kan dutse a jihar Naija.
Rachel ta wallafa wadannan hotunan a dandalinta da sada zumunta da muhawara inda ta bayya irin yanda tsohon shugaban yake birgeta saboda irin karamcinshi da kyawawan haleyenshi, da basira, da nutsuwa dake tattare dashi da kuma yanda yake sauraron mutane idan suna magana dashi, injita.
Haka dai wannan baiwar Allah tayi ta zuga tsohon shugaban kasar, kuma tace ita da tawagarta sun mikawa IBB din wani katin godiya da gaisuwa haka kuma ta kara da cewa abinda ya kara birgeta shine irin yanda ya dauki lokaci ya karanta katin da suka kai mishi.
Ha...