fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tag: labarin wasanni

Labarin Wasanni: An yanka ta tashi: Atletico Madrid ta ce bata yadda da cinikin Griezmann ba an cuceta dan haka zata je kotu

Uncategorized
Bayan sanar da sayen Antoine Griezmann da kungiyar Barcelona ta yi daga Atletico Madrid akan Yuro miliyan 120 a yau, Atletico Madrid ta bayyana cewa bata yadda da wannan ciniki ba kuma zata garzaya kotu. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labarin wasanni ya ci gaba da cewa, a sanarwat data fitar bayan cinikin, Atletico Madrid ta bayyana cewa asalin kudin da ta sawa Griezmann idan wata kungiya na son sayenshi Yuro miliyan 200 ne amma daga baya sai ta rageshi zuwa Yuro miliyan 120. Saidai Atletico Madrid tace Barcelona da Griezmann sun kammala ciniki tsakaninsu tun kamin ta ragewa dan wasan kudi, lura da irin alamun da dan wasan ya rika nunawa, kuma sun kammala wannan ciniki ne tun karshen kakar wasan data gabata. Dan haka Atletico Madrid tace ba ta yadda...

Labarin Wasanni: ‘Griezmann ya zama dan wasan Barcelona’

Uncategorized
Labarin wasanni da dumi-duminsu daga kasar Sifaniya na cewa Barcelona ta riga ta fitar da kudin sayan tauraron dan kwallon Atletico Madrid, Antoine Griezmann da suka kai Yuro miliyan 120 dan biya. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labaran wasanni na Sport English sun ce tuninan fitar da kudin abinda ake jira kawai shine Barcelona ta sanar da sayen dan wasan a hukumance. Labaran wasanni daga Marca kuwa na cewa, Griezmann ya riga ya zama dan wasan na Barcelona ma bayan dambarwar da aka sha akan sayen dan wasa wanda tun a shekarar 2017 Barcelonar ta so sayenshi dan ya maye mata gurbin Neymar amma yaki zuwa inda suka kare da sayen Ousmane Dembele. Hakanan Marca tace Barcelona ta bayyana cewa ba bashin kudin ta ci ba daga asusunta ta fito dasu amma ana s...

Labarin Wasanni: Ahmed Musa, Ighalo da Chidozie ba lafiya

Uncategorized
Me horas da 'yan wasan Najeriya Gernot Rohr ya bayyana matsalar rashin lafiya da kungiyar 'yan kwallon Najeriya, Super Eagles ke fuskanta ta matsalar rashin manyan 'yan wasan ta guda uku yayin da kungiyar ke shirin wasan kusa dana karshe a gasar ta neman cin kofin nahiyar Afrika kamar yanda labarin wasanni na yau suka nuna. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labarin wasannin sun ci gaba da cewa, Rohr ya bayyana Ahmed Musa, Odion Ighalo da Chidozie Awaziem a matsayin wanda ke fama da ciwuka a cikin kungiyar. Saidai yace, yana fatan 'yan wasan 3 zasu warke kamin Ranar Lahadi da Najeriya zata buga wasan kusa dana karshe da kasar Algeria

Labarin Wasanni:AFCON:Tunisia zata hadu da kasar Senegal a wasan kusa dana karshe

Uncategorized
Kasar Tunisia ta fitar da kasar Madagascar daga gasar cin kofin nahiyar Afrika a wasan da suka buga jiya inda ta saka mata kwallaye 3-0. Wannan na nufin kasar Tunisia ta kai wasan kisa dana karshe inda zata hadu da kasar Senegal. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Za'a buga wasannin na kusa dana karshe ne tsakanin kasashen biyu ranar Lahadi me zuwa da misalin karfe 5 na yamma idan Allah ya kaimu, kamar yanda labarin wasanni suka bayyana.

AFCON:Labarin Wasanni: Najeriya zata hadu da Algeria a wasan kusa dana karshe

Uncategorized
Labarin wasanni na yammacin nan ya bayyana cewa kasar Algeria da Kwadebuwa da suka buga wasan kusa dana kusa dana karshe a yau sun tashi kunnen doki 1-1 inda saida suka buga wasa na tsawon mintuna 120 amma babu wanda yayi nasara a wasan dalilin haka aka je bugun daga kai sai gola. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labarin wasanni ya ci gaba da cewa, an tashi wasan Algeriya nada nasara akan kwadebuwa da ci 4-3 a bugun daga kai sai gola da suka yi. Wannan na nufin Algeriar ta kai wasan kusa dana karshe kuma zata hadu da Najeriya a ranar Lahadi me zuwa in Allah ya kaimu.

Labarin wasanni: Ban ji dadin canja Ahmed Musa da Koc din Najeriya yayi ba>>Okocha

Uncategorized
Labarin wasanni na yau na cewa tsohon tauraron dan kwallon Najeriya, Jay Jay Okocha ya bayyana rashin jin dadinshi da canja Ahmad Musa da kocin Najeriya yayi yayin da ake mintuna 81 da wasa ya sako Moses Simon. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labarain wasannin ya ci gaba da cewa Okocha ya bayyana hakane bayan an tashi wasan da Najeriya ta ci kasar Afrika ta kudu 2-1. Yace Ahmed Musa ya zamarwa kasar Afrika ta kudu matsala a wasan saboda gudunshi, duk ya rikitasu, kwatsam sai koc ya fitar dashi ya sako Moses Simon, gaskiya ban ji dadin wannan canji ba saboda muhimmancin Ahmed Musa a wasan. Amma mu bamu isa mu ja da hukuncin Alkalin wasa ba, abin farin ciki shine Moses din ya bayar da taimako an ci kwallo. Dan haka kamata yayi idan mun yi nasara mu ...

Labarin Wasanni: Kalli yanda ‘yan kasar Dr Congo sukawa ministan wasannin su dukan kawo wuka saboda fitar dasu daga gasar cin kofin nahiyar Afrika

Uncategorized
Wani faifan bidiyo ya bayyana a shafukan sada zumunta wanda rahotanni suka nuna cewa ministan wasannin kasar Dr Congone, Huges Ngouelendele yake shan dukan kawo wuka a hannun 'yan kasar bayan da ya koma kasar bayan da aka fitar dasu daga gasar cin kofin Nahiyar Afrika daga matakin kasashe 16, kamar yanda labarin wasanni na yanzu ya nuna. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Kasar madagascar ce ta fitar da Dr Congo daga gasar. Labarin wasannin na ci gaba da cewa,an ga ministan na kokarin tsira da ranshi bayan da yaga alamun mutanen na kokarin kasheshi. Hoton bidiyon ya dauki hankula sosai inda da dama ke bayyana ra'ayoyi akai dake cewa indai wannan abu ya tabbata to kuwa lallai babu doka kasar kenan. Sannan kuma nan gaba watakila idan aka fitar da kasar...

Labarin Wasanni: Da wannan cin da Najeriya ta mana gara ace Egypt ta fitar damu>>Inji mawakin kasar Afrika ta kudu

Uncategorized
Labarin wasanni na jiya sun nuna yanda Najeriya ta fitar da kasar Afrika ta kudu daga gasar neman cin kofin Nahiyar Afrika da ci 2-1. Wannan abu be yiwa 'yan kasar Afrika ta kudun dadi ba inda har aka samu wani mawakin kasar da ake kira da AKA ya bayyana cewa da wannan cin da Najeriya ta musu ai dama kasar Egypt ce ta ciresu. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Labarin wasannin ya ci gaba da cewa, AKA ya bayyana wannan abune ta shafinshi na sada zumunta inda yace Najeriya sai yin nasara take akan Afrika ta kudu kan abubuwa da dama. Ya kuma kara da cewa, wannan wasa ba akan kwallo kawai ya tsaya ba, gasace da aka yi tsakanin kasashe kishiyoyin juna a nahiyar Afrika, abin akwai takaici, injishi kamar yanda labarin wasanni da hutudole.com yaci karo dashi ya ba...

Labarin Wasanni: Yanda Senegal ta kai ga wasan kusa dana karshe bayan cin Benin 1-0

Uncategorized
Labarin wasanni na yammacin yaudai ba zai kammalu ba idan ba a saka yanda kasar Senegal ta lallasa kasar Benin da ci daya me ban haushi ba a ci gaba da gasar neman daukar kofin nahiyar Afrika ba. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); An yi gumurzu inda har aka tafi hutun rabin lokaci babu wanda ya ci kwallo tsakanin kasahen, bayan dawowa daga hutun rabin lokacine sai Idrissa Gana Gueye na kasar Senegal ya ci mata kwallo ana mintin 70 da wasa kuma a haka aka tashi wasan. Kasar ta Senegal itace ta farko da ta fara kaiwa ga wasan kusa dana karshe a gasar sannan kuma labarin wasanni na hutudole.com ya samu na cewa wannan ne karin farko cikin shekaru 13 da kasar ke kaiwa ga wannan matsayi a gasar, rabonta da haka tun shekarar 2006.

AFCON:Labarin Wasanni:Najeriya ta kai wasan kusa dana karshe bayan cin Afrika ta kudu 2-1:Shugaba Buhari da Atiku sun tayasu murna

Uncategorized
Labarin wasanni da dumi-duminsu cikin darennan na cewa Super Eagles na Najeriya sun lallasa Bafana-Bafana na kasar Afrika ta kudu da ci 2-1 a wasan kusa dana kusa dana karshe da suka buga yau na neman daukar kofin Nahiyar Afrika dake gudana a Kasar Egypt. (adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Chukwueze ne ya fara ciwa Najeriya kwallo ana mintuna 27 da wasa amma hankalin 'yan Najeriya ya tashi yayin da kasar Afrika ta kudu ta rama kwallon ta hannun Zungu yayin da ake mintuna 71 da wasa. Saura minti 1 tal a tashi, dan wasan Najeriya, Troost-Ekong ya ciwa Najeriya kwallo ta biyu wanda a haka aka tashi wasan. Wannan nasara dai na nufin Najeriya ta kai wasan kusa dana karshe kenan a gasar. Chukwuezene aka baiwa gwarzon wasan saboda bajintar da ya nuna. Haka...