fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Lagos

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 71 sabuda keta dokar cutar Coronavirus

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 71 sabuda keta dokar cutar Coronavirus

Tsaro
Rundunar 'yan sandan jihar legas ta cafke a kalla mutane 71 sakamakon kin bin ka'idojin cutar Coronavirus a jihar. Sanarwar kamen na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi ya sanya wa hannu a ranar Talata. Adejobi ya bayyana cewa rundunar ta dakume mutanan ne a yankin Lekki da Surulere a yayin da wasu da rundunar ta ke zargi da hada fati wanda hakan ya sabawa dokar hana cunkosu wanda kuma hakan ya saba da dokar cutar Covid-19. Tuni kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada Umarnin Gurfanar da wadanda ake zargi.
Bidiyo: Wasu matasa sun karyata Rahotannin dake cewa an kashesu a Lekki Lagos

Bidiyo: Wasu matasa sun karyata Rahotannin dake cewa an kashesu a Lekki Lagos

Siyasa
Bayan harbe-harben da suka faru a Lekki dake Legas an watsa wasu Rahotanni dake cewa wasu matasa sun mutu.   Saidai matasan su 2 sun fito sun karyata wannan ikirari, dayan dan Fim ne wanda yace hotunan da akw watsawa nashi a wajan daukar wani fim ne aka daukesu.   Kungiyar Amnesty international dai ta yi zargin cewa mutane 12 ne aka kashe a harbe-harben na Lekki.   Kalli Bidiyon a kasa:   https://twitter.com/steveabbey_/status/1318913791237685249?s=19 https://twitter.com/Jub_rin/status/1318973416981057536?s=19
An Gano Gawar Wani Yaro Da Ceto Mutane 6 Yayin Da Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguje Legas

An Gano Gawar Wani Yaro Da Ceto Mutane 6 Yayin Da Bene Mai Hawa Uku Ya Ruguje Legas

Siyasa
An tabbatar da wani yaro ya mutu a lokacin da wani bene mai hawa uku ya rushe a kan titin Freeman, da ke tsibirin Legas. Olufemi Oke-Osanyintolu, darekta janar, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar Legas (LASEMA), wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar, ya ce ginin ya rushe ne a safiyar ranar Asabar yayin da mazauna gurin suke bacci. Ya ce, an ceto mutane shida daga rushen-shen ginin yayin da aka kai gawar yaran zuwa dakin ajiyar gawa. Oke-Osanyintolu ya ce, “Kungiyar ta amsa kiran gaggawa game da ginin da ya rushe a titin Freeman, da ke cikin tsibirin Lagos Island na jihar Legas". “Lokacin da aka isa wurin da abin ya faru da karfe 4 na safe, an gano wani bene mai hawa uku wanda ya fado kan mutane da ke barci a ciki. An kubutar da mutane shida  daga ginin da...
Za a rarraba wa daliban Legas rediyo don karatu daga gida

Za a rarraba wa daliban Legas rediyo don karatu daga gida

Siyasa
Gwamnatin Legas a Najeriya ta ce ta na shirin rarraba rediyo 10,000 ga dalibai domin karatu daga gida. Kwamishinar ilimi ta jihar Folashade Adefisayo ta ce jihar za ta yi hadin gwiwa da kamfanonin sadarwa wajen samar da intanet kyauta ga makarantu domin saukaka koyarwar ta intanet. A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sake bude makarantu ga daliban da ke ajin karshe a firamare da karama da kuma babbar sakandare domin ba su damar rubuta jarrabawar. Sai dai sauran daliban da ba a ajin karshe suke ba za su ci gaba da zama a gida. Gwamnatin ta Legas ta sanar da kudirin fara koyarwa ta rediyo domin tabbatar da cewa ba a bar daliban a baya ba a harkar karatunsu a wannan lokacin da ake fama da annobar korona. Ms Adefisayo ta ce gwamnatin ji...
A karin farko cikin awanni 24 ba’a samu karin wanda ya kamu da Coronavirus/COVID-19 a Legas ba saidai ta kashe mutum 2

A karin farko cikin awanni 24 ba’a samu karin wanda ya kamu da Coronavirus/COVID-19 a Legas ba saidai ta kashe mutum 2

Kiwon Lafiya
Alkaluman da hukumar kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar a jiya, Litinin sun bayyana cewa ba'a samu karin wanda suka kamu da cutar ba a jihar Legas, kwana daya bayan da aka samu mutane 70 da suka kamu da cutar.   Kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Akin Abayomi ya tabbatar da hakan inda yace saidai mutane 2 sun mutu sanadin cutar.   Yace daya daga cikin wanda suka mutun, namijine dan shekaru 45 wanda bai dade da dawowa daga kasar India ba.   Dayar kuma ta macece me shekaru 36 wadda bata da tarihin fita kasar waje ko ma'amala da wani wanda ya fita kasar waje ba. https://twitter.com/ProfAkinAbayomi/status/1252512948490289153?s=19   Jimullar wanda suka mutu sanadiyyar cutar Coronavirus/COVID-19 a jihar 16 kenan zuwa yanzu.
An sake sallamar mutane 6 da suka warke daga Coronavirus/COVID-19 a Legas

An sake sallamar mutane 6 da suka warke daga Coronavirus/COVID-19 a Legas

Kiwon Lafiya
Rahotanni daga jihar Legas na cewa an sallami karin mutane 6 da suka warke daga cutar Coronavirus,  kamar yanda gwamnan jihar, Babajide Sonwo Olu ya bayyana.   Gwamnan ta shafinsa na Twitter yace yawan jimullar mutanen da aka sallama bayan sun warke daga jihar sun kai 61 kenan.   1 daga cikin wanda aka sallama matane sai sauran 5 din kuma mazane.   Gwamnan yace ba zasu yi kasa a gwiwa ba har sai sun samu nasara akan wannan cuta, ya godewa mutanen jihar bisa hadin kan da suke bayarwa kan yaki da cutar.
Yanda Likitoci da malam jinya suka yi ta kansu bayan da aka kai marasa lafiyar da ake tunanin suna da Coronavirus/COVID-19 a Asibitin Legas

Yanda Likitoci da malam jinya suka yi ta kansu bayan da aka kai marasa lafiyar da ake tunanin suna da Coronavirus/COVID-19 a Asibitin Legas

Kiwon Lafiya
Wani lamari daya faru a Asibitin Gwamnati na Gbagada dake jihar Legas kan marasa lafiya na Coronavirus/COVID-19 da aka kai ya dauki hankula.   Wasu farar fatane tan kasar Misra/Egypt aka kai asibitin su 4 suna fama da rashin lafiya tsakar dare.   Daya daga cikinsu yana ta tari ba kakkautawa, kamar yanda wata majiyar Asibitin ta shaidawa jaridar Punch.   An kaisu Asibitinne a motar gida, koda likitoci da masu jiyya suka yi arba dasu, suka ga kuma fararen fata ne sai kowa yayi ta kansa suna fadin,"Coronavirus/COVID-19 ba da mu ba"   Likitocin sun kirawo masu gadin Asibitin nesa nesa suna gaya musu cewa a fitar da marasa lafiyar daga Asibitin dan nan ba gurin duba masu Coronavirus/COVID-19 bane.   Nan suma dai masu gadin suka yi ta masa s...