fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Lassa

A kalla mutane 244 ne suka rasa rayukan su a sakamakon cutar Zazzabin Lassa a shekarar 2020 – NCDC

A kalla mutane 244 ne suka rasa rayukan su a sakamakon cutar Zazzabin Lassa a shekarar 2020 – NCDC

Kiwon Lafiya
A rahoton da cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Kasa wato NCDC ta bayyana, tace An samu rahoton bullar cutar zazzabin Lassa a kananan hukumomi 131 dake jahohi 27 a fadin kasar, yayin da cutar a shekarar 2020 ta halaka mutane 244. Hakanan Cibiyar tace An samu adadin mutane 1,181 da suka kamu da cutar a dukkan jahohi 27 na kasar. Jihar Ondo ita ce jihar mafi samun adadin wadanda cutar ta salwantar da adadin mutune 83 sai jihar Edo da adadin mutum 40 tare da jihar Ebonyi mai mutane 23. A cewar hukumar jahohin Lagos, Ogun, Oyo duka an samu bullar cutar ammma babu wanda hukumar ta samu ya rasa ransa. Sauran jahohin da cutar ta bulla sun hada da Abia, Adamawa, Anambra, Bauchi, Benue, Borno, Delta, Enugu, FCT, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Nasarawa, Plateau, Rivers, Soko...