fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Lauretta Onochie

Gwamnati zata fara binciken masu bushasha da kudin da ba’a san inda suka samesu ba

Gwamnati zata fara binciken masu bushasha da kudin da ba’a san inda suka samesu ba

Siyasa
Mataimakiya ga shugaban Najeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yaƙar rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki ƴan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafuka sada zumunta. Ms Onochie ta shaida hakan ne a shafinta na Twitter ranar Litinin, tana mai cewa za a gayyaci irin wadanan mutane domin bincike kan yaɗa suka mallaki kadarorin da arzikin da suke nunawa. Onochie ta ce, "binciker yadda mutum ya ke rayuwarsa za ta kasance wajibi a Najeriya bisa sharuɗa na doka". Wannan na zuwa ne bayan a makon da ya gabata, shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya fitar da sanarwa cewa wajibi ne duk wani ma'aikacin banki ya bayyana kadarorin da ya mallaka. Onochie wrote, “Lifestyle Audit is now legal in Nigeria. Those who flaunt lifestyles t...
End SARS: CNN ta yiwa Duniya karya game da Najeriya>>hadimar Buhari, Onochie

End SARS: CNN ta yiwa Duniya karya game da Najeriya>>hadimar Buhari, Onochie

Siyasa
Lauretta Onochie, mataimakiya ta musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kafofin sada zumunta, ta soki gidan talabijin na CNN kan rahoton binciken da ya gudanar kan harbin Lekki, Legas.   A ranar Alhamis, hadimar ta bayyana cewa CNN ta yi wa kasashen duniya karya, ta kara da cewa Najeriya ba za ta ji tsoro ba.   “Ban ji haushi ba cewa CNN ta yi wa Duniya karya game da al’umman Najeriya. Ina cikin damuwa da suke tunanin har za mu haɗiye ƙaryarsu. Ba za a tursasa mu mu yarda da karya ba! ”, Ta wallafa a shafinta na Twitter. “I’m not upset that CNN lied to the world about my nation, Nigeria. I’m upset that they think we are so stupid that we will swallow their lies. We won’t be bullied into believing a lie!”, she tweeted.
Nadin Hadimar shugaba Buhari mukamin INEC: Kuma fa akwai membobinku dake aikin INEC>>APC ga PDP

Nadin Hadimar shugaba Buhari mukamin INEC: Kuma fa akwai membobinku dake aikin INEC>>APC ga PDP

Siyasa
Jam'iyyar APC ta mayarwa PDP martani kan caccakar da ta mata na maganar nada hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniyar INEC.   Tace itama fa PDP din na da mutanenta a cikin INEC inda ta bada misalin Dr. Johnson Alalibo wanda tace tsohon dan jam'iyyar ne amma a yanzu shine baturen INEC din a jihar Edo. Sannan shima shugaban INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu tsohon mai rike da mukamin gwamnati ne dan haka ya kamata indai rike mukamin gwamnati zai hana a baiwa mutum aiki a INEC PDP din ta yi kiran suma wadannan mutanen a soke nasu mukaman.   “President Muhammadu Buhari’s appointment of Lauretta Onochie as a National Electoral Commissioner for the Independent National Electoral Commission has been subject to rash, subjective, misplaced, and selec...
Bidiyo: Nada Lauretta Onochie mukamin INEC shiri ne na murde zaben 2023>>Wike

Bidiyo: Nada Lauretta Onochie mukamin INEC shiri ne na murde zaben 2023>>Wike

Siyasa
Gwamnan jihar Rivers,  Nyesom Wike yayi Allah wadai da nadin hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie a matsayin jami'ar hukumar zabe me zaman kanta.   Ya bayyana hakane a yayin ganawa da masu zanga-zanga jiya a kofar fadarsa bayan da suka je ganinsa.   Yace yayin da ake zanga-zangar ganin an kawo karshen SARS ya kamata a yi magana akan nadin da shugaban kasar yawa Hadimarsa Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniyar inda yace kuma a haka wai ake cewa INEC din ta zama me zaman kanta. https://www.youtube.com/watch?v=TWu2QFSzLR0 Yace wannan shirine na ganin an murde zaben shekrar 2023.
Kungiyoyin fafutuka 70 sunce basu yadda da nadin da Buhari yawa Hadimarsa, Lauretta Onochie a INEC ba

Kungiyoyin fafutuka 70 sunce basu yadda da nadin da Buhari yawa Hadimarsa, Lauretta Onochie a INEC ba

Siyasa
Kungiyoyin fafutuka 70 ne suka yi fatali da nadin da shugaba Buhari yawa hadimarsa, Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniyar hukumar zabe me zaman kanta, INEC yankin kudu maso kudu.   Kungiyoyin sun ce kundin tsarin mulki ya haramta nada wanda ke goyon bayan wata jam'iyya a cikin shuwagabannin INEC. Kungiyoyin sun ce Lauretta Onochie sananniyar me goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ce da kuma jam'iyyar APC dan haka suke kira da a gaggauta janye sunanta daga cikin wanda aka baiwa shugabanci a INEC din.   Shugaban gamayyar kungiyoyin,  Mr. Clement Nwankwo a wata sanarwa da suka fitar sun nemi majalisar tarayya ta yi watsi da sunan na Lauretta Onochie idan shugaban ya ki janye shi daga cikin wadanda zai baiwa mukamin na INEC sannan sun bukaci da a bincik...
Buhari ya nada Hadimarsa, Lauretta Onochie,matsayin kwamishiniya a hukumar INEC

Buhari ya nada Hadimarsa, Lauretta Onochie,matsayin kwamishiniya a hukumar INEC

Siyasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya turawa majalisar dattijai domin tantancewa tare da tabbatar da, mataimakiyar sa ta musamman kan kafofin watsa labarai, Lauretta Onochie a matsayin kwamishina ta kasa ta hukumar zabe mai zaman kanta, INEC. Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan a ranar Talata ya karanta wasikar da Shugaba Buhari ya tura sunan Onochie daga Delta tare da wasu Kwamishinoni uku na Kasa. Sauran sune farfesa Mohammed Sani daga jihar Katsina; Farfesa Kunle Ajayi daga jihar Ekiti da Seidu Ahmed daga Jigawa. Buhari ya ce “Nadin kwamishinoni na INEC yayi daidai da sakin layi na 14 na sashi na 11 na jadawalin farko na kundin tsarin mulkin 1999. The President, Major General Muhammadu Buhari (retd.), has asked the Senate to confirm the appointment of on...
Ba ka san girmama Manya ba>>Hadimar shugaba Buhari ta caccaki mawaki, Wizkid saboda sukar shugaban kasar

Ba ka san girmama Manya ba>>Hadimar shugaba Buhari ta caccaki mawaki, Wizkid saboda sukar shugaban kasar

Siyasa
Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ta caccaki mawaki, Wizkid inda ta bayyanashi da sakarai bayan caccakar da yawa shugaban kasan saboda matsalar 'yansandan SARS.   Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a shafi  Twitter ya yiwa shugaban kasar Amurka, Donald Trump fatan Allah ya bashi lafiya daga cutar Coronavirus data kamashi.   Saidai Wizkid ya mayarwa da shugaban kasar Martanin cewa Kai Tsoho, kaji da kasarta babu abinda ya shafeka da abinda ke faruwa a kasar Amurka,  'Yansanda na kashe mutane a kullun.   Saisai a martaninta, Lauretta ta bayyana Wizkid da cewa sakaraine, wata kila idan ya girma nan gana zai koyi girmama manya.   Ta kara da cewa, kiran wani da tsoho ba zagi bane amma yanda Wizkid din yayi ne babu alamar girmamawa a ciki. ...
A kasar Ingila, Kungiyar kwadago ce ke biyan ma’aikata su yi yajin aiki>>Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie

A kasar Ingila, Kungiyar kwadago ce ke biyan ma’aikata su yi yajin aiki>>Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie

Siyasa
A yau ne dai kungiyar Kwadago ta fasa yajin aikin da ta yi niyyar yi saboda karun kudin man Fetur dana wutar Lantarki saboda cimma matsaya da gwamnati.   Da take mayar da martani kan yajin aikin na kungiyar kwadago, me baiwa shugaban kasa shawara akan harkar kafafen sadarwa, Lauretta Onochie ta bayyana cewa banbancin yajin aiki a kasar Ingila da Najeriya shine. https://twitter.com/Laurestar/status/1310331788611538949?s=19 A kasar Ingila, Kungiyar Kwadago ce ke biyan ma'aikata su yi yajin aiki, kuma ba dole bane sai kowane maaikaci yayi yajin aikin ba, yayin da a Najeriya kuma Gwamnati ce ke biyan ma'aikatan duk da ana yajin aiki sannan kungiyoyin kwadagon su lakume hakkokin ma'aikatan.
Ku daina karawa Buhari yawan makiya, wanda yake dasu yanzu sun isa>>Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie

Ku daina karawa Buhari yawan makiya, wanda yake dasu yanzu sun isa>>Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie

Siyasa
Hadimar shugaban kasa, Lauretta Onochie ta bukaci 'yan Najeriya masu amfani da sunan shugaban kasar suna cimma burikansu su daina.   Tace musamman masu amfani da sunan shugaban kasar wajan aika abinda bai dace ba, tace su daina karawa shugaban kasar yawan makiya inda tace wanda yake dasu yanzu sun isa.   Ta kara da cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari mutum ne me bin doka da ota dan haka ba zai taba yadda ayi abinda ya sabawa doka ba.   Ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta.
Yanda PDP suka dauko Kasurgumin dan damfarar nan Hushpuppi ya taimaka musu cin zaben 2019>>Lauretta Onochie

Yanda PDP suka dauko Kasurgumin dan damfarar nan Hushpuppi ya taimaka musu cin zaben 2019>>Lauretta Onochie

Siyasa
Hadimar shugaban kasa me bashi shawara kan kafafen sada zumuntar zamani, Lauretta Onochie ta bayyana cewa PDP da mukarrabanta sun dauko Kasurgumin dan Damfarar nan Raymond Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi a lokacin da suke shirin yanda zasu lashe zaben 2019 dan ya taimaka musu cin zabe.   Lauretta ta bayyana hakane ta shafinta na sada zumunta inda tace Atiku Abubakar da Dino Melaye da Yakubu Dogara duk sun hadu da dan damfarar kuma akwai wani abu da suke boyewa kan abinda ya faru tsakaninsu da basa son gayawa 'yan Najeriya.   Ta kuma ce babu abinda ke boyuwa. Atiku Abubakar,  Bukola Saraki,  Da Yakubu Dogara duk sun nesanta kansu da wannan batu.