
‘Yan Matan Najeriya 94 da suka makale a kasar Lebanon sun dawo gida
Rahotanni daga jihar Legas na cewa 'yan matan Najeriya 94 da suka makale a kasar Lebanon sun dawo gida.
Hakan ya bayyanane bayan da aka ga 'yan matan ciki hadda wasu 30 da a baya aka gansu cikin wani Bidiyo a wani daki suna kiran gwamnati ta dawo dasu. Hutudole ya kawo muku rahoton a baya cewa wadannan mata sun je cirani amma sai matsin tattalin arziki yasa basu shiga kasar da sa'a ba.
Kasar Lebanon na fama da matsin tattalin arziki ga kuma cutar Coronavirus/COVID-19 ga kuma wasu bama-bamai da suka tashi wanda ya saka har gwamnatin kasar ta yi murabus.