fbpx
Tuesday, March 2
Shadow

Tag: Legas

Duk wanda yasan yayi hadari motarsa na tare damu ko wasu kayan Amfani yazo ya dauka nan da kwanaki 14 ko mu sayar dasu>>Yan Sandan jihar Legas

Duk wanda yasan yayi hadari motarsa na tare damu ko wasu kayan Amfani yazo ya dauka nan da kwanaki 14 ko mu sayar dasu>>Yan Sandan jihar Legas

Tsaro
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta gargadi jama’a, musamman wadanda suka yi hatsari da kuma masu motoci ko kayayyakin da aka ajiye su a wasu ofisoshin‘ yan sanda a duk fadin jihar da suje suyi bayani su karbi kayansu ko hukumar ta sayar da su. Rundunar 'yan sanda ta tsani yadda ganin motoci da sauran kayayyaki jama'a a cikin ofishoshinsu don haka take umartar Shugabannin rundunoni yan sanda da su ruguza kayan ba tare da bata lokaci ba. Bisa wannan umarnin, Rundunar Yan sanda ke kira ga jama'a wadanda ke da mota, mashi ko wani da su hanzarta suje suyi bayani su karbo kayansu nan da kwanaki 14, in ba haka ba zasu sayar da su.
Jihar Legas ta yi sa’ar samun Gwamnoni masu son ci gaba>>Gwamna El-Rufai

Jihar Legas ta yi sa’ar samun Gwamnoni masu son ci gaba>>Gwamna El-Rufai

Siyasa
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa jihar Legas ta yi sa'ar samun Gwamnoni masu son ci gaba.   Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a wani taron tattalin arziki da ya gudana A Jihar. Gwamnan yace Legas da kasa ce to zata zama itace kan gaba a kasashen Africa wajan tattalin arziki.   Yace ci gaban Legas na damfare da ci gaban Najeriya.  Gwamna El-Rufai yace jiharsa ta Kaduna na kwaikwayon Legas inda yace Legas din ce ta fara canja tsarin haraji kuma itama Kaduna ta bi sahunta.   Ya bayyana cewa zaau ci gaba da goyon bayan ci gaban jihar ta Legas.   “If Lagos were a country, it would have a bigger GDP than many African countries. For us in Kaduna state, Lagos is a model that we follow. You started the tax reform...
‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Maza 2 Da Ake Zargi da yin sojan gona a juhar Legas

‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Maza 2 Da Ake Zargi da yin sojan gona a juhar Legas

Tsaro
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta cafke wasu mutane biyu da aka bayyana sunansu da Ayan Okorie, dan shekara 45 da kuma wani mai suna Usman Ali, mai shekara 21 da haihuwa da ke lamba 51 a titin Ali Balogun, Ijora Oloye dake jihar Legas. ana zargin su ne da yin sojan gona wajan kiran kansu a matsayin jami'an soji da na 'yan sanda. Rahotanni sun rawaito cewa An kama wanda ake zargin ne a lokacn da suke  sanye da rigar kariya ta rundunar 'yan sanda da ke sashin Surulere. Bayan da aka tuhume su  sun Amsa laifin da cewa so ba jami'an tsaro ne na Gaskiya ba. Kwamishinan ‘yan sandan  jihar Legas, Hakeem Odumosu yayi tir da masu aiakta makamancin laifin.  
An kai fiye da yansanda 100 Lekki Toll Gate dan hana zanga-zangar SARS karo na 2

An kai fiye da yansanda 100 Lekki Toll Gate dan hana zanga-zangar SARS karo na 2

Siyasa
An jigbe jami'an 'yansandan Najeriya a Lekki Toll Gate awanni kadan kamin fara zanga-zangar SARS karo na 2.   Matasa sun sha Alwashin fitowa gobe dan fara zanga-zangar saboda nuna adawa da sake bude Lekki Toll Gate din duk da cewa ba'a hukunta wanda ake zargi da kashe masu zanga-zangar na farko ba.   Halan na zuwa ne duk da barazanar gwamnatin tarayya na cewa ba zata bari a yi zanga-zangar karo na 2 ba.
Hotuna: Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke mutane 19 da ake zargi da karya doka

Hotuna: Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke mutane 19 da ake zargi da karya doka

Crime
A ranar Lintinin din data gabata ne rundunar 'yan sandan jihar legas ta cafke wasu matasa kimanin 19 a jihar. Rundunar ta yi nasarar kwato makamai a hannun wadanda ta cafke da suka hada da Adduna da gatari da sauransu. Koda a rahotanni da muka kawo muku mun rawaito yadda rundunar ta cafke wasu bata gari a jihar a wani sumame da rundunar ta kai kan wasu da take zargin 'yan daba ne a jihar. A makonin nan dai rundunar 'yan sandan jihar ta kara kaimi wajan Dakile ayyukan bata gari a fadin jihar gaba daya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kai wani sumame maboyar bata gari inda ta cafke mutum 27

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kai wani sumame maboyar bata gari inda ta cafke mutum 27

Crime
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta kai wani samame maboyar masu aikata miyagun laifuka a jihar tare da cafke mutum 27 da ake zargi. Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar legas (PPRO) CSP Olumuyiwa Adejobi. A cewarsa Rundunar ta kai sumamen ne domin kakkabe ayyukan bata gari a jihar baki daya. Wadanda aka kame sun hada da Olajide Kolawole mai shekaru 26, Kehinde Ayoola, 25, Dola Abdullahi, 20, Michael Ogungbade, 19, da 23. Odumosu. Hakanan Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bada tabbacin cewa rundunar zata cigaba da himmatuwa wajan kakkabe ayyukan bata gari a dukkan sassan jihar.
Hadarin Mota Ya lakume rayukan mutane 5 A Jihar Legas

Hadarin Mota Ya lakume rayukan mutane 5 A Jihar Legas

Uncategorized
Hadarin Mota yayi sanadin salwantar rayukan mutane 5 A kan titin Ibadan zuwa Legas   Wani mummunan hadarin mota da ya afku a kan babban titin Legas zuwa Ibadan ya lakume rayukan mutane 5. Hadarin wanda ya faru a ranar Laraba, A cewar jami'an hulda da Jama'a na rundunar TRACE Babatunde Akinbiyi ya shaida cewa al'amarin ya rutsa da wata motar Mazda mai lamba LAGOS EPE 575 XA tare da wata Babbar mota mai lamba LAGOS APP 397 YA. An rawaito cewa, A kalla maza 4 ne hadi da Mace 1 suka rasa ransu a hadarin yayin da wanda suka samu raunuka aka aike dasu Asbiti.
Hukumar Hana fasakauri A Jihar Legas ta cafke Haramtattun magun guna

Hukumar Hana fasakauri A Jihar Legas ta cafke Haramtattun magun guna

Crime
Hukumar Hana fasakauri ta kasa reshan jihar Legas ta cafke wasu haramtattun Magun-guna wadanda suka hada da Taramadol da hukumar ta kirasu da ba su da rijistar da take nuna lokacin lalacewar su ba. A cewar hukumar ya zama wajubi a gareta data zafafa tare da sanya idanu wajan kame wadannan kayayyakin kasancewar suna da hatsari ga lafiyar 'yan Najeriya. Sanarwar hakan ta fito ne ta bakin Kwanturolan Hukumar Mohammed Abba-Kura wanda ya shaida hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai a jihar legas. A cewarsa, Magun-gunan da hukumar ta kama sam basa Dauke da shaidar wajan da ake hada su ballantana rijistar.  
Da Duminsa:Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan Legas in ya bashi Rahoto kan yanda za’a sake gina Legas din

Da Duminsa:Shugaba Buhari na ganawa da Gwamnan Legas in ya bashi Rahoto kan yanda za’a sake gina Legas din

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na ganawa da gwamnan Legas a fadarsa dake Abuja.   Hadimin shugaban, Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a ta shafinsa na sada zumunta, Sadai bai bada cikakken bayani kan ganawar shuwagabannin ba.   Amma Hutudole ya fahim ci cewa Gwamnan Legas din ya mikawa shugaba Buhari Rahoto ne kan yanda za'a sake gina Birnin Legas, wanda ba ya rasa nasaba da Asarar da Birnin ya tafka a yayin zanga-zangar SARS.   https://twitter.com/BashirAhmaad/status/1347164726044864513?s=19 PHOTOS: President Muhammadu Buhari receives in audience Lagos State Governor, H.E. Babajide Sanwoolu this afternoon, at the State House, Abuja.