fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Legos

Rundunar sojan ruwa ta ceto mutane 12 da jirgin ruwa ya kife dasu

Rundunar sojan ruwa ta ceto mutane 12 da jirgin ruwa ya kife dasu

Tsaro
A ranar Lahadin da ta gabata ne wasu sojojin ruwa suka ceto wasu mutane 12 da ke cikin wani kwale-kwale da ya kife a yankin Tarkwa Bay da ke jihar Legas. Jami’in yada labarai na rundunar sojan ruwa na Najeriya Thomas Otuji shine ya tabbatar da kubutar da mutane  a wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya raba wa manema labarai a ranar Litinin. Rundunar ta bayyana cewa, hatsarin wanda ya rutsa da mutane 12 ya faru ne a sakamakon igiyar ruwa wanda ta tilastawa jirgin kifewa.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Legas Sun cafke wasu Mutum 7 Da Ake Zargi ‘yan kungiyar asiri ne

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Legas Sun cafke wasu Mutum 7 Da Ake Zargi ‘yan kungiyar asiri ne

Crime
Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas sun cafke wasu mutane bakwai da ake zargi‘ yan kungiyar asiri ne a yankin Ikorodu na jihar. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan  jihar (PPRO), SP Olumuyiwa Adejobi, shine ya shaida hakan, A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a jihar.  Rundunar ta bayyana sunayen wadanda ake zargin a matsayin Abolaji Adebayo, mai shekaru 21; Josiah Offem, 37; Oluwapelumi Oyeyinka, 25; Lamidi Taofeeq, 41; Ahmed Shittu, mai shekaru 48; Rabiu Ganiyu, 25; da Zainab Nurudeen, mai shekaru 20, mace tilo a cikinsu. A cewarsa, wadanda ake zargin 'yan kungiyar asirin sun kai wa' yan banga hari don daukar fansar kama wani mamban su da kungiyar "Agbekoya" ta yi. A karshe Kwamishina 'yan sandan jihar Hakeem Odumosu, ya umarci da a mika batun zuwa bangaran bi...
Gwamnan Jihar Legas Babajide yace zai soke biyan tsaffin Gwamnonin Jihar kudin fansho

Gwamnan Jihar Legas Babajide yace zai soke biyan tsaffin Gwamnonin Jihar kudin fansho

Uncategorized
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu yace zai soke biyan tsaffin Gwamnoni da mataimakansu a Jihar kudin fansho. Gwamnan Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a wani kudiri da ya gabatar ga majalisar dokokin jihar. A wani Labarin kuma Rundunar Yan Sandan Najeriya ta karyata wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta game da karin albashin jami'anta, inda ta bukaci Jama’a da suyi watsi da labarin. Idan kuma muka leka kasashan ke tare,  Zababben Shugaban Kasar Amurka Joe Biden yace rashin amincewar Donald Trump da faduwa a zabe abun kunya ne.  
“Rufe Boda Ne Ya Jefa Ni Harkar Sace Sace – cewar Wani Barawo Da Rundunar ‘yan sanda ta kama

“Rufe Boda Ne Ya Jefa Ni Harkar Sace Sace – cewar Wani Barawo Da Rundunar ‘yan sanda ta kama

Tsaro, Uncategorized
Wani barwo da a ka bayyana da suna Ifeanyi Odo mai shekaru 42 ya shaidawa  hukumar 'yan sanda a jihar legas cewa, sakamakon rufe boda ne ya jefa shi harkar sace sace. A cewasa, kafun rufe boda yana yin Sana'ar shigu da sabulai daga kasar Ghana zuwa Najeriya amma a sakamakon rufe boda da gwamnati tai yasa ba zai iya ci da kanshi ba hakan ne ya sanya shi yake balle shaguna domin ya tsira da abin da zaici. Dubun Odo ta cika ne tare da abokin harkarsa mai suna  Onyebuchi Chidozie mai shekaru 39 a ranar 4 ga watan Ogusta  bayan da rundunar 'yan sanda ta gano talabijin din da suka sata. Haka zalika ana zargin cewa sun sace wayoyi da gwala gwalai na ma kudan kudade.
Mutane 10 sun mutu hudu sunyi batan dabo bayan da wani jirgin ruwa ya kife a jihar Legas

Mutane 10 sun mutu hudu sunyi batan dabo bayan da wani jirgin ruwa ya kife a jihar Legas

Kiwon Lafiya
An tabbatar da mutuwar mutane kimanin 10 yayinda 4 sukai batan dabo bayan da wani jirgin ruwa ya kife a jihar legas a ranar Juma'a data gabata. A wata sanarwa dauke da sa hannun Darakta Janar na Hukumar Kula da Ruwa na Jihar Legas (LASWA), Oluwadamilola Emmanuel a ranar Juma'a, hukumar ta ce jirgin ruwan ya bar Kirikiri dauke da fasinjoji 19. Wani daga cikin wadanda suka tsira  ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne a dai dai lokacin da mai aikin kula da tukin jirgin ya shagaltu wajan karbar kudi daga hannun fasinjoji a yayin da a ke tafiya. A cewar Hukumar LASWA ta bayyana cewa tuni ta danka matukin jirgin wajan 'yan sanda domin gudanar da bincike. Haka zalika ya tabbbatar da cewa harzuwa yanzu hukumar na binciken wadanda sukai batan dabo.
Rundunar ‘yan sandan jihar legas  ta cafke wani matashi da ya sumbaci ‘yar karamar yarinya kuma ya watsa bidiyon a kafar sadarwa

Rundunar ‘yan sandan jihar legas ta cafke wani matashi da ya sumbaci ‘yar karamar yarinya kuma ya watsa bidiyon a kafar sadarwa

Tsaro
An cafke matashin ne mai suna Oluwatosin Babtunde da laifin sumbatar wata 'yar karamar yarinya kuma ya watsa bidiyon a kafar sadarwa. Oluwatosin dalibi ne, dake karatu a Jami'a a jihar legas. Lamarin dai ya farune a ranar 2 ga watan yuni na shekarar 2020, a shagamu dake jihar legas. Matsahin dai an zarge shi da laifin sumbatar karamar yarinya kuma ya dora shi a kafar sadarwa, sai dai a cewar kakakin rundunar 'yan sandan jihar legas Bala Elkana ya bayyana cewa kwamishinan 'yan sanda Hakeem Odumosu yaga bidiyon matashin inda ya bada umarnin yin bincike tare da cafke matashin. Bayan bincike da hukumar 'yan sanda ta gudanar tai nasarar Kama matashin, inda kuma rundunar ta mikia shi ga hukumar bincike ta CID A cewar matashin jimkadan bayan sakin bidiyon yayi martanin cewa shi ba ...