fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Leicester City

Wolves 0-0 Leicester City: yayin da Leicester City ta rasa damar kamo United a teburin Premier League

Wolves 0-0 Leicester City: yayin da Leicester City ta rasa damar kamo United a teburin Premier League

Uncategorized
Kungiyar Leicester City ta rasa damar daidaita makin tada Manchester United a saman teburin gasar Premier League bayan da suka tashi wasa babu ci tsakanin suda Wolves. Gabadaya kungiyoyin sun damarmakin zira kwallo a wasan amma sai dai a karshe sun raba maki bayan da suka tashi 0-0. Hutudole ya samo cewa, Sakamakon wasan yafi bakanta ran tawagar Bredan Rodgers saboda ta rasa damar kamo Manchester United, yayin da ita kuma Wolves taji dadin makin guda duba rashin nasarar tayi a wannan kakar. Wolves 0-0 Leicester City: Bredan Rodgers miss the chance to level on point with Manchester United. Leicester City missed the chance to climb level on points with Manchester United as they drew 0-0 with Wolves at Molineux and stay third in Premier League standings. Both sides had chances ...
Zorya Luhansk 1-0 Leicester City: yayin da Leicester ta rasa damar kasanewa a saman Group G na gasar Europa League

Zorya Luhansk 1-0 Leicester City: yayin da Leicester ta rasa damar kasanewa a saman Group G na gasar Europa League

Wasanni
Kungiyar Leicester City ta rasa damar kasancewa a saman teburin Group G na gasar Europa League, bayan Allahyar Sayyadmanesh yaci kwallo ana daf da tashi wasa wadda tasa Zorya Luhansk tayi nasarar lallasa ta 1-0. Leicester City ta rigada ta cancanci buga wasannin karshe na gasar amma bata kai hari mai kyau a wasan ba har saida aka kai minti na 80,wanda hakan ne yaba kungiyar Zorya damar bata kashi ta hannun Sayyadmanesh. A karshe dai sakamakon wasan yasa yanzu Leicester sai tayi nasarar cin wasanta da AEK Athens a filin King Power idan har tana so ta kasance a saman Group G din.
Leicester City 1-2 Fulham, Torino 2-2 Sampdoria: yayin da Fulham taci kwallaye biyu tun kafin aje hutun rabin lokaci karo na farko tun shekara ta 2012

Leicester City 1-2 Fulham, Torino 2-2 Sampdoria: yayin da Fulham taci kwallaye biyu tun kafin aje hutun rabin lokaci karo na farko tun shekara ta 2012

Uncategorized
Kungiyar Fulham tayi nasarar cin kwallaye biyu tun kafin aje hutun rabin lokaci karo na farko a gasar Premier league tun a shekara ta 2012, a wasan da suka lallasa kungiyar Bolton 3-0. Yayin da shi kuma Ivan Cavaleiro ya zamo dan wasa na farko daya ciwa Fulham penariti tun bayan da Aleksandar Mitrovic yaci masu a watan satumba, yayin da suka barar da ganadaya ukun da suka buga kafin yau. Jamie Verdy ne ya taimakawa Bernes ya ramawa Leicester kwallo guda wanda hakan yasa yanzu gabadaya kwallaye hudu da Leicester taci Fulham suka fito ta hannun dan wasan bayan daya ci biyu kuma ya taimaka wurin cin biyu. Kungiyar Torino da Samdoria kuwa sun raba maki a gasar Serie A bayan da suka tashi 2-2 a wasan da buga yau.
Liverpool 3-0 Leicester City: yayin da Diogo Jota ya zamo dan wasan Liverpool na farko da yayi nasarar cin kwallo a wasanni hudu na gida daya fara bugawa kungiyar a tarihi

Liverpool 3-0 Leicester City: yayin da Diogo Jota ya zamo dan wasan Liverpool na farko da yayi nasarar cin kwallo a wasanni hudu na gida daya fara bugawa kungiyar a tarihi

Wasanni
Kungiyar Liverpool tayi nasarar lallasa Leicester City daci uku ta hannun dan wasan Leicester Evans da kuma gwarazan yan wasan guda biyu wato Diogo Jota da kuma Roberto Firmino. Nasarar da Liverpool tayi tasa yanzu taci wasanninta na gida guda 64 a jere karo na farko a tarihin ta yayin da shi kuma dan wasanta Diogo Jota ya zamo dan wasa na farko da yayi nasarar cin kwallo a wasanni hudu na gida daya fara bugawa kungiyar a tarihi. Kungiyar Leicester City kuwa ta fadi wasanni har guda uku tsakanin tada Liverpool tunda Bredan Rodgers ya farya jagorancin kungiyar kuma kwallaye tara ne Liverpool tayi nasarar zira masu a gabadaya wasannin. Ta bangaren Serie A kuwa Bevento tayi nasarar cin Fiorentina 1-0 yayin da Inter Milan ta lallasa Torino 4-2 sai Roma taci Parma 3-0, sannan Sampd...
Leicester City ta dare saman teburin Premier League bayan lallasa Wolves da 1-0

Leicester City ta dare saman teburin Premier League bayan lallasa Wolves da 1-0

Wasanni
Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta lallasa Wolverhampton Wanderers da ci 1-0 a wasan gasar Premier League da suka buga da yammacin yau, Lahadi.   Jamie Verdy ne ya ciwa Leicester City kwallo a bugun Penareti wanda kuma ya sake samun wani bugun amma ya barar. Wannan yasa Leicester City ta dare saman teburin gasar Premier League. A yanzu Verdy babu kungiyar dake buga gasar Premier League da bai ci kwallo ba.
Manchester United zasu tayar mana da hankali>>Kocin Leicester City

Manchester United zasu tayar mana da hankali>>Kocin Leicester City

Wasanni
Manajan Leicester City Brendan Rodgers ya bayyana cewa Manchester United zasu fi tayar da hankulan su akan tawagar shi idan suka tashi buga wasa gobe a filin King Power, saboda su United ba wai son wasan kawai suke ba bukatar wasan suke. Kungiyar Leceister City suna kokarin gama wannan kakar a cikin kungiyoyi hudu na saman teburin gasar premier lig, amma sai dai wasanni biyu kadai suka ci cikin wasannin su guda takwas da suka gabata bayan sun dawo daga hutun watanni uku saboda cutar korona. Leicester City zasu buga wasan su na karshe a wannan kakar da Manchester United kuma Manchester sun fisu da maki guda. Rodgers ya bayyana cewa sun ji dadin wannan kakar wasan saboda sun samu cigaba bayan sun gama kakar bara a na tara cikin teburin gasar premier league. Rodgers ya kasance ...
Leicester City 2-0 Sheffield United: Leicester sun kara samun karfin gwiwa wurin cancantar shiga gasar Champions League

Leicester City 2-0 Sheffield United: Leicester sun kara samun karfin gwiwa wurin cancantar shiga gasar Champions League

Wasanni
Kungiyar Leicester City sun huce fishin su akan Sheffield United bayan Bournemouth sun basu kashi ranar lahadi. Dan wasan su Thomas mai shekaru 19 shine ya taimakawa Ayoze Perez wurin cin kwallon data sa suka fara jagorantar wasan. Golan Sheffield United Dean Henderson yayi nasarar cire kwallaye da dama a wasan amma ya kasa cire kwallon Demarai Gray wadda tasa Leicester suka yi nasarar lashe gabadaya maki uku na wasan kuma suka wuce Manchester United da maki uku wanda suka kasance na biyar a teburin gasar. Hari mai kyau daya kacal Sheffield United kai kuma sun rasa samun cancanta a gasar zakarun nahiyar turai mai zuwa su kuma Leceister suka yi nasarar komawa na hudu a teburin, Sheffield sun kasance na takwas a saman teburin gasar da maki 58 kuma Tottenham da maki daya suka wuce s...
Coronavirus/COVID-19: An killace ‘yan kwallon Leicester 3

Coronavirus/COVID-19: An killace ‘yan kwallon Leicester 3

Wasanni
An samu alamun cutar Covid-19 a tattare da wasu yan wasan leicester city guda uku sun kuma killace kansu da kansu yayin da aka kebance su da sauran yan wasan kungiyar inji Bredan Rodgers. Rodgers bai tabbatar da cewa akwai sauran yan wasan dake dauke da cutar Covid-19 ba amma ya kara da cewa kulob din zasu bi sharuddan cutar na killace kai. Yan kungiyar ta Foxes suna da wasan premier League tsakanin su da Watford ranar sati. Rodgers Yace akwai wasu kadan daga cikin yan wasanmu da aka samu alamun cutar atattare dasu. Ya Kara da cewa abin kunya ne ace an daga wasan mu da Watford duk da cewa lafiyar jama'a tafi komai. Ya tambaya shin za'a buga wasan ne batare da yan kallo ba, dama wasa ya kunshi abubuwa guda biyu yan kallo da masu bugawa idan daya daga cikin su bayana...