
Yanda Lemun Tsami ke illa ga Al’aurar Mata
Al'aurar 'ya mace wuri ne mai matukar haɗari da ke bukatar kulawa ta musamman saboda irin tsarin halittar da aka yi mata.
Wuri ne mai daukar cuta cikin hanzari, sannan ya yaɗa ta cikin sauki.
Don haka a baya iyaye da kakanni ke cewa a yi amfani da wasu abubuwa irinsu lemon tsami domin tsaftace ta daga wari da kuma kamuwa da cutuka.
Sai dai da zuwan kimiyya an samar da wasu sinadaren da akan iya wannan aiki da su ba tare da haifar da illa ga al'aurar mata ba ko kuma mahaifarsu, a cewar Dakta Fatima Abdulahi wata kwararriya kan sha'anin cutukan mata da ke aiki da kungiyar Marie Stopes International a birnin tarayyar Abuja.
Alakar lemon tsami da al'aurar mata
Dakta Fatima ta ce a kimiyyance a jikin kowanne abu akwai sinadarai irin s...