fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Tag: Leonel Messi

Messi yaci kwallo ta 700 yayin da Ronaldo ke da 728

Messi yaci kwallo ta 700 yayin da Ronaldo ke da 728

Wasanni
A wasan da Barcelona ta buga da Atletico Madrid a daren jiya wanda ya kare da sakamakon 2-2, Leonel Messi wanda shine ya ci kwallo ta 2 kuma wadda itace kwallonshi ta 700 ya bi sahun babban abokin takararshi, Cristiano Ronaldo inda suka zama su kadaine masu buga kwallo a yanzu da ke da yawan kwallaye 700.   Messi ya ci wadannan kwallayene a wasanni 862 inda ya ciwa kungiyarshi kwallaye 630 sai kuma kasarshi da ya ciwa kwallaye 70. Saidai har yanzu Real Madrid ke a saman teburin La Liga da tazarar Maki 1.
A yau Leonel Messi ke murnar cika shekaru 33: karanta kaji wasu daga cikin muhimman tarihin Messi

A yau Leonel Messi ke murnar cika shekaru 33: karanta kaji wasu daga cikin muhimman tarihin Messi

Wasanni
A yau tauraron Argentina da Barcelona lionel Messi yake murnar cika shekaru 33 a rayuwar sa. An haifi Messi a ranar 24 ga watan yuni shekara ta 1987 a garin Rosario kuma ya fara yin wasa a kungiyar Barcelona yana dan shekara 13. Tun daga lokacin da Barcelona suka siya Messi ya zamo daya daga cikin zakarun yan wasan kwallon kafa na duniya, kuma ya kafa tarihi da dama a wasannin kwallon kafa. Mutane da yawa sun taya Messi murnar zagayowar ranar haihuwar shi yayin da suma Barcelona da La Liga suka taya shi murnar. Wasu daga cikin muhimman tarihin Messi: A lokacin yarintar Messi, ya kasance yana da wata cuta kuma zakarun kasar Spain din suka biya aka yi mai tiyata bayan su siye shi. Messi ya zamo dan wasan daya fi cin kwallaye masu yawa a Barcelona a shekara ta 2014. Lionel Mess...
Bidiyo:Kalli yanda Messi ya ture dan wasan Sevilla amma bai samu jan Kati ba

Bidiyo:Kalli yanda Messi ya ture dan wasan Sevilla amma bai samu jan Kati ba

Wasanni
Barcelona sun buga wasa tsakanin su da Sevilla a daren jiya kuma sun tashi wasan 0-0 yayin da Messi ya kirkiri abun yin sharhi a wasan tun kafin aje hutun rabin lokaci. Dan wasan Argentinan ya samu matsala da Carlos yayin da aka kusa tashi wasan kuma anga shi ya bugi dan wasan Sevillan a fuska. Babu wani hukuncin da aka dauka akan kaftin din Barcelonan, kuma masoyan wasan kwallon kafa suna ta tambayar alkalin wasan a kafafen yada zumunta dalilin da yasa bai bashi Cati ba. https://twitter.com/HamzaAm38567805/status/1274184561556099073?s=19 https://twitter.com/DaddyAgu/status/1274100449386409986?s=19 Yayin da wani mutun yake cewa Wato shi Messi zai nushin wani mutun ba tare da an bashi yalan kati ba kenan?, wani kuma yace shin Messi zai iya nushin wani mutun a fuska alkalin wasa ...
Messi ya amince zai kara tsawon kwantirakin shi izuwa 2023

Messi ya amince zai kara tsawon kwantirakin shi izuwa 2023

Wasanni
Kaftin din Barcelona Lionel Messi ya shirya kara tsawon kwantirakin shi bayan ya samu matsala da shuwagabannin kungiyar tashi a kwanakin baya. Messi ya bukaci wata yarjejeniya a cikin kwantirakin wadda zata iya as shi ya bar kungiyar a kyauta a karshen wannan kakar wasan. Amma yanzu dan wasan Argentinan ya amince zai kara tsawon kwantirakin nashi izuwa 2023. Messi ya buga gabadaya wasannin shi a kungiyar Barcelona kuma ana sa ran a kungiyar zai yi ritaya, sai dai in ya koma kungiyar shi ta yarinta ta Nwell Old Boys. Manema labarai na Mundo Deprotivo suma sun tabbatar da cewa Messi zai kara tsawon kwantirakin nashi izuwa 2023, kuma dan wasan zai iya barin kungiyar kafin wa'adin kwantirakin nashi ya cika. Messi yana jin dadin wannan kakar wasan tare da kungiyar shi ta Barcelon...
Javier Tabas: Shugaban La Liga ya bayyyana cewa tafiyar Ronaldo bata shafi La Liga ba amma tafiyar Messi ka iya shafar gasar

Javier Tabas: Shugaban La Liga ya bayyyana cewa tafiyar Ronaldo bata shafi La Liga ba amma tafiyar Messi ka iya shafar gasar

Wasanni
Masoyan Cristiano Ronaldo da Lionel Messi baza su taba daina yin musu akan cewa waye gwarzon yan wasan kwallon kafa a tsakanin jaruman nasu ba. Ronlado da Messi sun ci kwallaye dayawa a wasannin kwallon kafa kuma sun samu kyaututtuka  daban-daban fiye da shekaru goma da suka gabata. Amma Ronaldo ya bar Madrid a shekara ta 2018 ya koma Juventus, kuma hakan ya kawo karshen gasar da suke yi tsakanin shi da tauraron Barcelona Messi. Tunda Ronaldo ya koma Juventus Madrid suke shan fama wajen lashe wasu kofuna a shekaru biyu da suka gabata. Duk da haka dai shugaban La Liga Javier Tabas ya bayyanawa manema Labarai na RAC1 cewa koda ace tafiyar da Ronaldo yayi ta shafi Madrid, to baza ta shafi La Liga ba saboda sun dade suna hidima wa gasar tasu. Amma Messi daban ne saboda shine tauraron
Barcelona 2-0 legenes: Messi yayi nasarar cin penariti a saukake amma Barca basu yi kokari sosai a gidan nasu ba

Barcelona 2-0 legenes: Messi yayi nasarar cin penariti a saukake amma Barca basu yi kokari sosai a gidan nasu ba

Wasanni
Kungiyar leganes sun yi kokari sosai lolacin da aka da a buga wasan kuma sun barar da kwallaye har guda biyu masu kyau cikin minti 15. Baya kinyi 30 kuma Barcelona suka fara yin wasa da kwallon yayin da Ansu Fati yayi nasarar jefa kwlo daya kafin aje hutun rabin lokaci. Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin kuma Barcelona sun cigaba da wasa da kwallon amma basu yi kokari sosai ba. Lionel Messi ya ruga da kwallon yayin da yayi nasarar samun penariti wadda yaci a saukake. Riqui Piug ya shigo filin da kuzari amma sai wasan ya kare. Nasarar da Barcelona tayi yasa sun kerewa abokan hamayyar su wato Madrid da maki biyar, Amma wasan nasu bai nishadantar ba duk da cewa sun yi nasarar tashi 2-0.
Daga dawowar La Liga har Messi ya kafa sabon tarihi

Daga dawowar La Liga har Messi ya kafa sabon tarihi

Wasanni
Kwallon da Kaftin din Barcelona Lionel Messi yaci ranar sati yayin da suke karawa da Mallorca tasa ya kafa sabon tarihi a gasar La Liga. Dan wasan Argentina shi yaci kwallon su ta karshe wadda tasa suka tashi a 4-0. Kwallon tasa dan wasan mai shekaru 32 ya zamo dan wasa na farko da fara cin kwallaye 20 a kakar wasanni guda 12 a jere, ya fara wannan kokarin tun kakar wasan 2008-09 yayin daya ci kwallaye 23 a kakar wasan. Jiya suma abokan hamayyar su Madrid suka yi nasara akan Eibar yayin da suka tashi 3-1. Messi ya taimakawa Martin Braithwaite da Jordi Alba wurin cin kwallayen su bayan Arthur ya zamo dan wasan daya fara zira kwallo cikin raga a wasan. Har yanzu dai Barcelona sune a saman teburin gasar yayin da suka wuce Madrid da maki biyu.
Bidiyo: Messi ya ci kwallo 1 a wasan da Barcelona ta ci Mallorca 4-0

Bidiyo: Messi ya ci kwallo 1 a wasan da Barcelona ta ci Mallorca 4-0

Wasanni
A daren yaune Barcelona ta buga wasa da Real Mallorca a ci gaba da gasar cin Kofin La liga. Vidal ne ya fara ciwa Barca kwallo ana mintuna 2 da rake wasa inda Braithwaite ya saka kwallo ta 2 ana mintuna 37 da wasa, wadda Messi ya bashi taimakonta, kuma itace kwallonsa ta farko da ya ciwa Barcelona.   Kalli bidiyon kwallon tasa: https://twitter.com/simplyfutbal9/status/1271905704337477632?s=19 Jodi Alba ya ci kwallo ta 3 bayan da dawowa daga hutun rabin lokaci ana mintuna 79 da take wasa sai kuma Messi da yaci kwallo ta 4 ana mintunan karshe. Bayan kwallon da yaci,Messi shine ya bayar da taimako akaci kwallaye 2 a wasan na yau.   Kalli bidiyon kwallon da Messin ya ci a kasa https://twitter.com/MessiCF10/status/1271924821815787520?s=19 Da wannan yana da jimi...
Samuel Eto’o: Ya kamata Messi ya ci gaba da wasa har sai ya kai shekaru 70

Samuel Eto’o: Ya kamata Messi ya ci gaba da wasa har sai ya kai shekaru 70

Wasanni
Samuel Eto'o ya kasance gwarzon yan wasan nahiyar Afrika a tarihi kuma ya samu damar yin wasa a kungiyar Real Madrid, daga baya kuma ya koma Barcelona. Kuma yayi nasarar lashe gasar champions lig har sau biyu. Bayan shekaru hudu kuma, Samuel ya kara samun damar lashe kofin gasar champions lig a karo na uku, yayin daya koma kungiyar Inter. Marca sun tambaya Samuel cewa shin yana tunanin Barcelona sun dogara akan Messi ne?. Sai yace haka yake. Messi shine zakaran yan wasan kwallon kafa na duniya baki daya, kuma a koda yaushe yana tambaya Messi cewa shin waya ke so yayi aiki tare da shi. Kowace kungiya a duniya tana son Messi saboda haka ya kamata a bashi goyon baya. Ya kara da cewa a yanzu Messi ba zai iya yin gudu ba kamar karamin yaro mai shekaru 25 ba, koda yake yana yin h...
Setien:Messi yana cikin koshin lafiya kuma ba zai samu wata matsala ba

Setien:Messi yana cikin koshin lafiya kuma ba zai samu wata matsala ba

Wasanni
Kaftin din Barcelona Lionel Messi bai hallaci atisayi ba na wasu kwanaki yayin daya ke yin nashi atisayin daban saboda yana fama da rauni. Amma kochin kungiyar Quique Setien bai damu da wannan matsalar ba. Setien ya gayawa Movistar cewa ba Messi kadai bane wannan matsalar ta faru da shi ba, wasu abokan aikin shi suma basu yi atisayin ba saboda suna da rauni kuma matsalar Messi ba gagaruma bace. Yace yana tunanin Messi yana cikin koshin lafiya kuma ba zai samu wata matsala ba, haka suma sauran yan wasan. Saboda haka zasu tsaya suga yadda gasar zata kasance. Setien yace suna da wasanni da dama amma basu da yawa a tawagar su kuma tabbas a koda yaushe yana so yaga Messi a fili idan suna buga wasa.