fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: Leroy Sane

Bayern Munich ta kammala shirin karbar dan wasan kungiyar Manchester City na Ingila Leroy Sane

Bayern Munich ta kammala shirin karbar dan wasan kungiyar Manchester City na Ingila Leroy Sane

Wasanni
Hakan zai faru ne a karkashin wani tsari na musanya. Leroy Sane dan asalin kasar Jamus ya jima bai taka leda ba tun a watan Agustan da ya gabata bayan da ya samu rauni a gwiwarsa. Sai dai rahotanni sun ce har yanzu ba su daddale a kan ko nawa Bayern Munich za ta biya Manchester City a kan wannan musaya ba. Amma dai wasu na cewa ko nawa aka ba Manchester City za ta karba tun da a yanzu tana cikin matsalar rashin kudi saboda annobar coronavirus. Wannan musaya dai na zuwa ne yayin da a wannan Laraba gwamnatin Jamus da gwamnoni 16 na jihohin kasar ke ganawa don duba yiwuwar bude wasannin Bundesliga a cikin wannan wata.