fbpx
Friday, October 23
Shadow

Tag: Lionel Messi

Mourinho: Messi ya amince da komawa Chelsea a shekara ta 2014

Mourinho: Messi ya amince da komawa Chelsea a shekara ta 2014

Wasanni
Maganar da Messi yayi na barin kungiyar Barcelona a kakar data gabata ta girgiza duniyar wasan kwallon kafa sosai, amma sai dai ba kowa ne yasan cewa wannan bashi ne karo na farko da dan wasan Argentinan ya bukaci barin kungiyar ba. Dan jarida na kasar Italiya Gianluca Di Marzo ya bayyana cewa kiris ya rage Messi ya koma kungiyar Chelsea a shekara ta 2014 wadda Barcelona ta kasa lashe babban kofi a kakar karkashin jagorancin Gerardo Martino, wanda ya taimakawa kungiyar ta lashe kofin Spanish Super Cup amma aka cire ta a gasar Champions League kuma ta fadi wasannin karshe na La Liga da Copa del Rey a hannun Atletico da kuma Real Madrid. Dan jaridar ya kara da cewa Messi ya gana da Jose Mourinho a lokacin kuma har dan wasan mai shekaru 33 ya amince da komawa Chelsea wadda take shirin b...
Mun tanadi kudin siyen Messi a kaka me zuwa>>Manchester City

Mun tanadi kudin siyen Messi a kaka me zuwa>>Manchester City

Wasanni
Lionel Messi yayi kokarin barin kungiyar Barcelona a kakar data gabata domin ya koma kungiya Manchester City, amma sai dai dan wasan ya fasa komwa gasar Premier League din saboda makudan kudaden Barcelona ta bukata wurin siya da tauraron nata. Sauran mayan kungiyoyin wasan kwallon kafa kamar Juventus da Paris Saint german sun bayyana ra'ayin su na siyan Messi amma Manchester City ce ake sa ran zasu yi nasarar siyan dan wasan a lokacin saboda dangantakar shi da kocin kungiyar Pep Guardiola, kuma City yai kokarin shawo kan shuwagabannin Barca ta siyar masu da Messi amma sun ki amincewa. Saboda haka yanzu Manchester City zata jira nan da shekara daya domin ta siya dan wasan a kyauta. Manema labarai na GOAL sun bayyana cewa daya daga cikin manyan shuwagabannin Manchester City ya bayyan...
Farashin Messi ya sakko kasa da yuro miliyan 100 karo na farko tun shekara ta 2012

Farashin Messi ya sakko kasa da yuro miliyan 100 karo na farko tun shekara ta 2012

Wasanni
Lionel Messi yana cikin shekarar karshe na kwantirakin shi da Barcelona wanda hakan yasa farashin dan wasan a kasuwar yan wasa ya sakko kasa da yuro miliyan 100 karo na farko a cikin shekaru takwas da suka gabata. Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau shida ya kasance daya daga cikin gwarazan yan wasan kwallon kafa na duniya saboda nasarorin da dan wasan ya samu a kungiyar Barcelona. Kuma shi da Ronaldo sun mamaye duniyar wasan kwallon kafan fiye da shekaru goma da suka gabata yayin da suka zira kwallaye masu dunbin yawa kuma taimaka wurin cin wasu kwallayen. Messi da Ronaldo sune yan wasan mafiya tasada na duniya a cewar kasuwar yan wasa yayin da farashin Messi ya kasance kusan yuro miliyan 162 a shekara ta 2018, amma yanzu kasuwar ta saki sabon farshin yan wasan La Liga k...
Messi ya taimakawa Argentina tacoi Ecuador 1-0 a wasan cancanta na gasar kofin duniya

Messi ya taimakawa Argentina tacoi Ecuador 1-0 a wasan cancanta na gasar kofin duniya

Wasanni
Lionel Messi ya fara cimma burin shi na lashe kofin duniya a yau bayan ya taimakawa Argentina ta lallasa Ecuador 1-0 a wasan cancanta na buga gasar kofin duniya mai zuwa. Dan wasan ya shashantar da rikicin da Barcelona take ciki domin ya mayar da hankalin shi wa kasar Argentina a lokacin da kasar take bukatar tallafin shi saboda kar ta kara fadi wasa a hannun Ecuador karo na biyu bayan taci su 2-0 a shekaru hudu da suka gabata. Kuma dan wasan mai shekaru 33 bai ba kasar tashi kunya ba bayan daya ci penari a minti na 13 wadda tasa aka tashi wasan 1-0.
Babban burina a yanzu shine na lashe kofin duniya da kasar Argentina>>Messi

Babban burina a yanzu shine na lashe kofin duniya da kasar Argentina>>Messi

Siyasa
Tauraron dan wasan kwallon kafa na duniya,Lionel Messi zai dauki hutu daga kungiyar sa ta Barcelona domin ya taimakawa kasar Argentina ta lashe kofin duniya a Qatar wanda kuma hakan ka iya zama damar shi ta karshe da zai kokarta ya lashe kofin. Dan wasan mai shekaru 33 wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau shida ya lashe dukkan wasu kofuna wasan kwallon kafa na kungiya a Barcelona da kuma kyaututtuka amma bai taba samun nasara a kasar  Argentina ba. Messi ya bayyana cewa "babban burina a yanzu shine na lashe kofin duniya tare da kasar Argentina". Babbar damar da Messi ya taba samu a gasar shine a 2014 yayin da kasar Jamus ta basu kashi a wasan karshe na gasar kuma wasan su da Ecuador ranar alhamis ne zai bashi damar fara shirye shiryen buga gasar. Messi zai cika shekaru 35 yayin
Shugaban Atletico ya bayyana cewa zai siya Messi domin ya cigaba da wasa tare da Suarez

Shugaban Atletico ya bayyana cewa zai siya Messi domin ya cigaba da wasa tare da Suarez

Wasanni
Kungiyar Atletico Madrid zata tarbi Lionel Messi da hannu biyu idan har yanzu dan wasan yana so ya cigaba da aiki tare da tsohon abokin aikin shi na kasar Uruguay Luiz Suarez a cewar shugaban Atletico Enrique Cerezo. Suarez ya bar Barcelona a makon daya gabata a farashin yuro miliyan 5.5 kuma hakan ya bakanta ran babban abokin shi Messi. Lionel Messi, wanda a makonnin da suka gabata ya bayyana cewa Barcelona ta hana shi tafiya a wannan kakar ya kalubalanci shuwagabannin kungiyar shi da suka siyar da Suarez yayin da har Neymar ya bashi goyon baya a jawabin daya yi na siyar da dan wasan a Instagram. Kuma shugaban Madrid din yanzu ya bayyana cewa zai siya Messi idan har yana so ya cigaba da wasa da Suarez. Luiz Suarez ya fara buga wasan shi na farko a Atletico Madrid ranar lahadi ku...
Messi ya kerewa Ronaldo inda ya zama dan wasa na daya mafi Daraja a Duniya

Messi ya kerewa Ronaldo inda ya zama dan wasa na daya mafi Daraja a Duniya

Wasanni
Zakarun yan wasan kwallon kafan guda biyu sune suke kasancewa a saman lissafin manyan yan kasuwa na wasannin duniya kafin dan wasan Basketball LeBron James sai kuma tauraron Indiya na wasan Criket Virat Kohli, amma wannan karin abin ya ba mutane mamaki saboda tauraron Barcelona ya kerewa abokin hamayyar shi na Juventus. Cristiano Ronaldo shine yake zuwa na farko a cikin manyan yan kasuwa na wasannin duniya kuma shine yafi kowa mabiya a kafar sada zumunta ta Instagram yayin da mabiyan suka kai miliyan 238 shi kuma Messi ya keda miliyan 167, amma Messi shine yafi gabadaya yan wasa lashe kyautar Ballon d'Or. SportPro suna yin amfani da yawan mabiya da kuma karuwar masoya da darajar dan wasan a kafafen sada zumunta da kuma kwantirakin kamfanoni da dai sauran su wurin zabar babban dan...
A Karon Farko: Cristiano Ronaldo da Messi basa cikin gwarazan yan wasan UEFA

A Karon Farko: Cristiano Ronaldo da Messi basa cikin gwarazan yan wasan UEFA

Wasanni
Cristiano Ronaldo da Lionel Messi basa cikin jerin takaitaccen sunayen gwarazan yan wasan shekara na UEFA karo na farko cikin shekaru goma da suka gabata, bayan zakarun yan wasan sun kasa haskakawa a gasar zakarun nahiyar turai na kakar data gabata. Tauraran yan wasan Munich guda biyu Robert Lewandowski da kuma Manuel Neuer suna cikin lisafin sai kuma dan wasan tsakiya na kungiya na kungiyar Manchester City Kevin De Bryuyne. Tauraron dan wasan Barcelona Messi ya lashe kyautar UEFA sau biyu sannan kuma sunan shi ya fito a cikin jerin sau shida a shekaru goma da suka gabata, Yayin da shi kuma zakaran Juventus Cristiano Ronaldo ya lashe kyautar ta UEFA sau uku sannnan kuma sunan shi ya fito a cikin jerin takaitattun gwarazan yan wasan shekara sau tara a cikin shekaru gom da suka gabata....
Neymar ya baiwa Messi goyon baya a jawabin daya yi na siyar da Suarez

Neymar ya baiwa Messi goyon baya a jawabin daya yi na siyar da Suarez

Wasanni
Tauraron dan wasan Paris Saint German na kasar Brazil, Neymar ya ba Messi goyon baya akan sukar shuwagabannin Barcelona daya yi a kafar sada zumunta ta Instagram bayan kungiyar ta siyarwa Atletico Madrid da Luiz Suarez bayan ya kasance a kungiyar na tsawon shekaru shida. Yayin da Messi yake turawa Suarez sakon bankwana ta Instagram, dan wasan Argentinan ya soki kungiyar tashi bayan daya bayyana cewa Suarez bai cancanci Barcelona ta yada shi ba bayan ya kasance daya daga cikin manyan yan wasan ta na tarihi kuma shima Neymar ya kara da cewa yana mamakin yadda Barcelona take gudanar da al'amuranta. Messi da Suarez da kuma Neymar sun kasance manyan abokai yayin da suke buga wasa tare a Barcelona har ake yi masu inkiya da MSN kafin Neymar ya koma PSG a shekara ta 2017. Shima tsohon dan ...
Abinda Barcelona taiwa Suarez bai kamata ba>>Messi

Abinda Barcelona taiwa Suarez bai kamata ba>>Messi

Wasanni
Lionel Messi ya soki kungiyar shi ta Barcelona bayan ta siyar da tauraron dan wasan ta Luiz Suarez wa Atletico Madrid wanda kuma hakan yake kara tabbatar da cewa har yanzu yana nan kan bakar shi na barin kungiyar. Messi yaso barin Barcelona amma shi kungiyar ta hana shi tafiya saboda haka zai zira sai kaka mai zuwa sannan ya bar ta kyauta. Barcelona ta ta bar wasu yan wasan ta sun bar kungiyar kamar Rakitic da Vidal da dai sauran su. Sabon kocin Barcelona Koeman duk shine yayi wannan aikin kuma ya bayyanawa Luiz Suarez cewa baya cikin tsarin shi na Barcelona wanda hakan yasa ya koma kungiyar La Liga ta Atgletico Madrid. Messi da Suarez sun kasance aminan juna sosai amma yanzu Barca ta karya wannan abotar dake tsakanin su. Messi yayi jawabi gami da tafiyar Suarez a shafin shi na I...