
Liverpool tasha kashi karo na farko a shekarar 2022 bayan Inter Milan ta doke ta daci 1-0 a gasar zakarun nahiyar turai
Kungiyar Livepool tasha kashi a karin farko shekarar 2022 bayan da Inter Milan ta doke ta daci 1-0 a wasan na biyu na zagayen kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar turai.
Amma duk da haka Liverpool ce tayi nasarar kaiwa zagayen gaba a gasar domin ta doke Milan daci 2-0 a wasan farko da suka buga.
Lautaro Martinez ne ya ciwa Milan Milan kwallo guda a wasan kuma sunyi kokari sosai, amma babban cikas din da kungiyar ta samu shine jan katin da aka baiwa Sanchez wanda shine ya rage masu kwarin gwiwa.