Gidan Limamin Loko Kenan Da Tsohon Sarkin Kano Sanusi II Ya Kwana Kafin A Kai Shi Garin Awe Dake Jihar Nasarawa A Yau.
Bincike ya nuna cewa layin glo ne kadai yake aiki a kauyen da aka ajiye tsohon Sarkin.
Bayan sauke sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II daga karagar mulki da gwamnatin Abullahi Ganduje ta yi a jiya, yanzu sarkin yana jihar Nasarawa inda zai yi zaman Hijira.
Mai martaba sarkin Loko, Alhaji Abubakar Ahmad Sabo ya shaida wa wakiliyar mu Zainab Babaji cewa daga Kano aka kai sarkin zuwa karamar hukumar Loko inda zai zauna zuwa wani lokaci.
A cewarsa bai san tsawon lokacin da Sarki Sanusi II zai yi a Nasarawa ba, gwamnati ce zata yanke wannan hukuncin.
Ya ce "bai kamata a kawo sarki Sanusi nan ba, sabo da Loko ya yi kauye da yawa. A ganina ba zasu barshi ya dade a nan ba, kafin su canza masa waje.", kamar yanda VOA ta ruwaito.
Tun Jiya dai ‘yan Najeriya ke ta mayar da martani kan wannan batu da ya sami Sarki Sanusi II, inda da y...
Rahotanni daga jihar Narasawa sun tabbatar da cewa garin Loko na jihar ne aka kai Sarki Muhammad Sanusi da gwamnatin Kano ta tsige, Kamar dai yanda muka labarta muku a jiya.
Hadimin gwamnan Kano,Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana cewa karfe 3n dare Sarkin da tawagar da ta rakashi suka sauka a Loko dake Jihar ta Nasarawa.
Ya kara da cewa wanda suka wa Sarkin Rakiya Tuni suka kama hanyarsu ta Komawa Gida Kano.
https://www.instagram.com/p/B9i4EfdFEcl/?igshid=jr9wzrhbtcua