
An kama ‘yan Luwadi 2 a Jihar Jigawa
Kwamandan Hisbah na jihar Jigawa, Malam Ibrahim Dahiru ya bayyana cewa sun kama wasu matasa 2 da ake zargi da Luwadi a birnin Dutse.
Yace sun samu kirane daga jama'a inda suka je suka kama Adamu me shuekaru 32 da Abokinsa, da ya fito dag Unguwa 3 dake Kano da kuma Tijjani me shekaru 20 da ya fito daga Jihar Sokoto.
Hutudole ya fahimci matasan sun hadu ne ta shafin Facebook inda Adamu yawa Dahiru dadin bakin zai bashi Dubu 50 idan ya yadda yayi luwadi dashi, sun hadu inda suka kama otal suka kwana. Saidai da gari ya waye, Adamu ya kasa cika alkawari, a nanne fa sai rikici ya kaure.
Hayaniyar da suke ce tasa mutane suka ji abinda ke faruwa kuma suka sanar da jami'an Hisbah. Wanda ake zargi dai sun amsa Laifinsu kuma za'a mika su wajan 'yansanda.