fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Madigo

Biyon ‘yar Madigo na rokon abokiyar Lalatarta data tuba karta barta:Na sai miki mota dan faranta miki rai, me kika gani a wajen Namiji?

Biyon ‘yar Madigo na rokon abokiyar Lalatarta data tuba karta barta:Na sai miki mota dan faranta miki rai, me kika gani a wajen Namiji?

Uncategorized
Bidiyon wasu 'yan Madigo ya watsu sosai a shafikan sada zumunta inda aka ga daya daga ciki wadda kamar itace magajiyar na rokon abokiyar masha'ar tata cewa kada ta barta.   An jita tana gaya mata cewa na sai miki mota dan kimin abinda nake so amma banga abinda kika hango a wajan Namiji ba kike son barina.   Ita dai wadda ta tubar taki tsayawa inda ta kama gabanta tace aure zata je ta yi, an ji magajiyar ta na cewa ina sonki.   Wasu Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya farune a kasar Ghana, kalli Bidiyon a kasa:  
Bidiyo:An saki bidiyon tallar Fim din Madigo na farko da ka yi a Najeriya

Bidiyo:An saki bidiyon tallar Fim din Madigo na farko da ka yi a Najeriya

Uncategorized
Fim din me suna Ife an tallatashi ne a shafin YouTube inda wadda ta yishi, Pamela Adie ta kasance tana fafutukar ganin cewa 'yan Madigo da Luwadi sun samu 'yanci a Najeriya. Saidai Fim din da wuya hukumar tace fina-finan Najeriya ta amince a fitar dashi. Dalilin hakane Pamela tace zata sakeshi a yanar gizo ta yanda kowa da kowa daga kowane sashe na Duniya zai iya kallo. https://m.youtube.com/watch?v=uZeGMw_urCU Fim din dai shime na farko da aka yi irinshi a Najeriya. A baya kasar Kenya ta hana fitar da fim irinshi da aka yi na farko a kasar.
Kasar Montenegro ta amince ‘yan Luwadi da Madigo su yi soyayya

Kasar Montenegro ta amince ‘yan Luwadi da Madigo su yi soyayya

Uncategorized
Kasar Montenegro ta amince da dokar data baiwa 'yan Luwadi da Madigo damar yin soyayya. Saidai har yanzu kasar bata amince da auren jinsin ba.   Kasar na kokarin ganin ta shiga tarayyar Turai. Saidai a shekarar 2013 a wani bincike da aka yi, ya nuna cewa kaso 70 cikin 100 na 'yan kasar na kyamar Luwadi da Madigo saboda ra'ayin 'yan mazan jiya. Saidai Rahoton kamfanonin Dillancin labaran AFP ya bayyana cewa sabon binciken da aka yi ya nuna cewa karamar kasar me mutane 650,000 a yanzu rabin mutanen ta na ganin cewa ana takewa masu Madigo da Luwadi hakkinsu.   Jam'iyyar DPS ta shugaba, Milo Djukanovic na goyon bayan wannan mataki.
Ba zamu taba daina hukunta masu luwadi da Madigo ba saboda neman tallafi daga kasashen yamma>>Kasar Gambia

Ba zamu taba daina hukunta masu luwadi da Madigo ba saboda neman tallafi daga kasashen yamma>>Kasar Gambia

Siyasa
Kasar Gambia wadda yawanci Musulmai ne suka fi yawa a cikinta, ta jaddada matsayar ta ta cewa ba zata amince da Luwadi da Madigo ba.   Hakan na zuwane bayan wasu rade-radin dake yawo kwanannan cewa kasar na shirin sassauta hukuncin da akewa masu luwadi da Madigo dan neman tallafi daga kasashen Yamma. Ebrima Sankare wanda shine me magana da yawun gwamnatin kasar ya bayyana cewa ba gaskiya banr labaran dake cewa suna shirin amincewa da Luwadi  kasar dan neman tallafin kasashen yammaba, ya bayyana kalaman da cewa na siyasane kawai dan samun karbuwa a wajan mutane, kamar yanda kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito.   Yace ko sake duba dokar ba zasu yi ballantama su canja ta saboda Luwadi ya sabawa al'adun mutanen kasar.
Matashiya ta kashe Abokiyar yin madigonta data kama tana “cin amanarta da Namiji”

Matashiya ta kashe Abokiyar yin madigonta data kama tana “cin amanarta da Namiji”

Uncategorized
'Yansanda a jihar Delta sun kama wata matashiya me suna Spicykvng Vee wadda ake zargi da kashe wata data bayyana a matsayin budurwarta da suke madigo tare.   Spicykvng ta kashe Vivian kuma ta tsallake ta gudu zuwa Enugu inda makwautane suka ji wari ya ishesu inda da aka bincika sai aka ga gawar Vivian. Labarai 2 sun bayyana kan dalilin kisan Vivian, kamar yanda Punch ta ruwaito inda labarin farko ke cewa, Vivian ta kama Spicykvng tana cin amanarta da namiji wanda hakan ya hadasu fada.   Labarai na biyu kuma na cewa mahaifiyar Vivian ce bata son tarensu da Spicykvng wanda hakan ya saka rashin jituwa tsakaninsu har ta caka mata wuka tana cikin bacci.   Me magana da yawun 'yansandan jihar, Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun...
An kama matan da ake zargi da auren junansu a Sokoto

An kama matan da ake zargi da auren junansu a Sokoto

Auratayya
Hukumar Hisbah ta Jihar Sakkwato ta kama wadansu mata biyu da ake zargin sun yi auren junansu (auren jinsi)  suna zaune tare tsawon wata hudu. Hukumar na kuma zarginsu da shaye-shayen miyagun kwayoyi a Unguwar Obalande a Karamar Hukumar Sakkwato ta Kudu da ke Jihar Sakkwato.   Kwamandan Hukumar ta Jihar, Dokta Adamu Bello Kasarawa wanda ya jagoranci jami’ansa zuwa  kamen, ya shaida wa Aminiya cewa “Wannan lamari da muke ji a wasu wurare ya zo mana nan, mace ta auri jinsinta, duk wanda ya ji haka zai yi mamaki yadda al’umma ke kara lalacewa. Matan sun yi alkawarin ba rabuwa a tsakaninsu ta hanyar sanya zobe da shan jinin juna don kara alakar.”   Ya ce: “Bincikenmu ya gano sun fara alaka da juna ne tun a Jihar Kaduna, kuma akwai wadanda suka sanya su cikin lamarin.”...