Jami'an hukumar zabe me zaman Kanta, INEC sun yiwa shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu kyakkyawar tarba bayan da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tabbatar dashi a matsayin shugaban hukumar karo na 2.
Jam'iyyar PDP ta gayawa Shugaban hukumar zabe me zaman kanta, INEC, Mahood Yakubu da ya je kasashen Amurka da Ghana dan koyo yanda ake zaben Gaskiya.
Kakakin PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Yace kasar Ghana ta samar da yanayin zabe me kyau wanda abin koyi ne, hakanan kasar Amurka ma ta samar da da yanayin zaben da aka yi shi me cike da sarkakkiya amma baa sa jami'an tsaro sun hana mutane 'yancinsuba.
Ya kara da cewa da shekaru 2 da suka rage zuwa kamin a fara zaben shekarar 2023, ya kamata INEC ta saka masi ruwa da tsaki cikin al'amuranta dan gudanar da zaben gaskiya.
“The INEC Chairman should initiate processes and procedures that will guarantee prompt arrival of ballot materials, rapid accreditation and v...
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya rubuta wasika zuwa ga majalisar dattijai don neman amincewa don tabbatar da Farfesa Mahmoud Yakubu a karo na biyu a matsayin shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC).
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar a ranar Talata a lokacin da za a ci gaba da harkokin majalisa bayan hutun wata guda.
A cikin wasikar, Shugaba Buhari ya nemi ‘yan majalisar da su hanzarta yin la’akari da bukatarsa ta karin wa’adin shekaru biyar ga Mahmoud a matsayin Shugaban INEC.