fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Tag: Majalisa

Tsaf za’a iya tsige Shugaba Buhari>>’Yan Majalisa

Tsaf za’a iya tsige Shugaba Buhari>>’Yan Majalisa

Siyasa
Yan majalisar wakilai na PDP sun mayarewa shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado Doguwa martani kan cewa da yayi za'a dakatar da shugaban marasa rinjaye, Kinsley Chinda kan barazsnar da yayi ta tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari.   'Yan PDP irinsu, Mr. Awaji Abiante, Farah Dagogo, Tajudeen Yusuf duk sun bayyana goyon baya ga Chinda inda suka ce ra'ayin 'yan Najeriya ya fada.   Sannan kuma sun bayyana cewa babu wanda zai iya dakatar dashi, saboda mutanensa ne suka zabeshi ya je majalisar ya wakilcesu, dan haka babu maganar cewa wai wani zai datakar dashi, abinda ya fada akan doka yake. “part of the sycophancy that is killing Nigerian democracy,” adding that the “wishful thinking antagonises the rising concern of Nigeria citizens.” According to ...
Majalisa ta sake yin kira ga Buhari ya kori shuwagabannin tsaro

Majalisa ta sake yin kira ga Buhari ya kori shuwagabannin tsaro

Tsaro
Majalisar Dattijai ta sake yin kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya kori shuwagabannin tsaro dan canjasu da wasu.   Wannan matsayi da majalisar ta dauka ya biyo bayan maganar da Kashim Shattima ya taso da ita.   Shattima ya bada Misali da kashe-kashen da aka yi kwanannan a Borno. Majalisar ta kuma bukaci shugaban kasar da ya baiwa jami'an tsaro kayan aiki yanda suka kamata kuma na zamani.   A baya dai majalisar ta taba yin irin wannan kira a shugaban kasar ya ki amincewa.    
Dalilin da yasa ba zamu iya bincikar ‘yan majalisar dake da hannu a kamuyamuyar NDDC ba>>Majalisa

Dalilin da yasa ba zamu iya bincikar ‘yan majalisar dake da hannu a kamuyamuyar NDDC ba>>Majalisa

Siyasa
Kwamitin dake kula da bin ka'idar aiki na majalisar Dattijai ya bayyana cewa dalilin da yasa ba zai iya bincikar 'yan majalisa da ake zargi da hannu a karbar kwangiloli a maaikatar kula da yankin Naija Delta ta NDDC ba shine saboda babu isassun bayanai akan lamarin.   Ministan ma'aikatar,  Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana sunayen 'yan majalisar inda yace an basu aikin kwagilar wanda an biya wani kaso daga ciki amma sun yi watsi da aikin ba tare da an kammala ba. Hutudole ya kawo muku cewa wasu daga cikin 'yan majalisar sun karyata ikirarin na sanata Akpabio saidai duk da haka majalisar ta kafa kwamiti na musamman akan wannan lamari. Sanata Ayo Akiyeleru wanda shine ke kula da harkar binciken ya bayyana cewa basu samu isassun bayanan da za su yi binciken akai ba. Dali...
Zamu ci gaba da kokarin ganin mun fahimtar da shugaba Buhari cewa ya kamata ya kori shuwagabannin tsaro>>Majalisa

Zamu ci gaba da kokarin ganin mun fahimtar da shugaba Buhari cewa ya kamata ya kori shuwagabannin tsaro>>Majalisa

Tsaro
Majalisar dattijai ta bayyana cewa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan ci gaba da ganin ta fahimtar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari muhimmancin korar shuwagabannin tsaro.   Hakan na zuwane duk da yunkuri na farko da majalisar ta yi na gayawa shugaban kasar ya canja shuwagabannin tsaro bai yi nasara ba. Hutudole ya fahimci a ranar 21 ga watan Yuli ne Sanata Ndume ya kawo wani kudiri inda ya koka kan yawan matsalar tsaro inda yace sojoji ma basu tsira ba ana ta kashesu, farar hula kuwa baa san iyakar wanda aka kashe ba. Bayan bayanin Sanata Ndume, Sanata dake shugabantar kwamitin Kwastam ya bukaci da a kori shuwagabannin tsaron kuma majalisar ta Amince da haka. Hutudole ya ruwaito muku cewa  a tare da bata lokaci ba, shugaba Buhari ya mayarwa da majalisa martanin cewa shi k...
Itama dai Ministar Kudi zata bayyana gaban Majalisa saboda zargin rashin bada isassun kudi kan aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano

Itama dai Ministar Kudi zata bayyana gaban Majalisa saboda zargin rashin bada isassun kudi kan aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna da Kano

Siyasa, Uncategorized
Majalisar tarayya ta gayyaci Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad da Ministan Ayyula, Raji Fashola da babban akanta Janar, Ahmad Idris da 'yan kwangilar dake aikin gina manyan tituna a fadin kasarnan su bayyana a gabanta. Majalisar na son ganin wadannan mutanene saboda wasu kudade da ta ce an samu gibinsu data gano. Sannan majalisar ta bayyana cewa a shekaru 2 da aka yi ana aikin gina Titunan Kano zuwa Kaduna da Abuja da kuma na Legas zuwa Ibadan sunga cewa dala Miliyan 300 kawai aka bayar wanda ya kamata ace an bayar da isassun kudi idandai ana son kammala aikin akan lokaci. Shugaban Kwamitin majalisar dake binciken, Olamilekan Adeola ne ya bayyana haka inda yace bayanan da suka samu daga wajan gwamnati basu gamsar ba.
Majalisar Dattawa ta bukaci a sauke hafsoshin tsaron Najeriya

Majalisar Dattawa ta bukaci a sauke hafsoshin tsaron Najeriya

Tsaro
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi kira ga manyan hafsoshin tsaron Najeriya su ajiye muƙamansu a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a ƙasar. Sanata Ali Ndume ne ya gabatar da ƙudurin a lokacin zaman majalisar na ranar Talata. A cewar Sanata Ndume, ya gabatar da kudurin ne saboda irin yadda aka yi wa sojoji kwanton-ɓauna a Katsina inda aka kashe da dama daga cikinsu. Sannan kuma ga wasu sojoji da suka yi murabus daga aiki. A cewar Sanata Ndume waɗannan batutuwan biyu na da matukar tayar da hankali.
Majalisa ta bada Umarnin a kamo mata Shugaban NDDC da ya fice daga dakin taro yayin da take mai tambaya akan Gibin Biliyan 143

Majalisa ta bada Umarnin a kamo mata Shugaban NDDC da ya fice daga dakin taro yayin da take mai tambaya akan Gibin Biliyan 143

Siyasa
Mwamitin majalisar wakilai dake kula da harkokin Naija Delta ya fitar da sanarwar a kamo masa Daraktan hukumar Naija Deltan, NDDC, Farfesa Kemebradikumo Pondei wanda ya fice daga dakin taron da suke masa tambayoyi a yau 16, ga watan Yuli.   A jiyane dai Daraktan ya bayyana a gaban majalisar inda ya kasa amsa tambaya kan wasu kudi Biliyan 143 da aka samu gibinsu a kasafin kudin ma'aikatar na shekarar 2019. Yace a bashi lokaci tukuna. Da ya koma wajan tambayoyin a yau, Alhamis sai ya bayyana cewa ba zai iya yon bayani kan kudin ba. Sannan kuma ya nemi da zai fita daga dakin taron, ba tare da ya jira amsa daga wajan 'yan Majalisar ba, ya fice daga dakin taron.   Hakan yasa majalisar ta nemi da a kamo matashi ruwa a jallo.
A karshe dai Gwamnatin tarayya ta fara daukar matasa 774,000 aiki, duk da kin amincewar Majalisa

A karshe dai Gwamnatin tarayya ta fara daukar matasa 774,000 aiki, duk da kin amincewar Majalisa

Uncategorized
Gwamnatin tarayya ta sanar da fara daukar matasa aiki wanda za'a dauki matasa Dubu 1 a kowace karamar hukuma 774 ta kasar nan.   Gwamnatin ta sanar da hakane ta shafinta na sada zumunta inda tace ta kaddamar da daukar matasan aiki da kuma saka shafin da za'a ga wakilan da zasu yi wannan aiki a jihohi. A baya dai mun kawo muku yanda Karamin Ministan Kwadago Festus Keyamo ya bayyana cewa shugaba Buhari ya bashi umarnin ci gaba da daukar aikin ba tare da amincewar Majalisa ba.