fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: Majalisar Kano

Dambarwar tsige sarkin Kano: ‘Yan majalisar dokokin Jihar Kano da aka dakatar sun dawo zama bayan hukuncin kotu

Dambarwar tsige sarkin Kano: ‘Yan majalisar dokokin Jihar Kano da aka dakatar sun dawo zama bayan hukuncin kotu

Siyasa
Wakilai biyar da aka dakatar a majalisar dokokin jihar Kano, a ranar Talata, sun sake dawowa majalisar bayan da wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta ba da umarnin a barsu su cigaba da gudanar da aikin su na majalisa. Daya daga cikin mambobin kwamitin da aka dakatar, Bello Butubutu, memba mai wakiltar mazabar Tofa / Rimin Gado, ya shaidawa manema labarai bayan kammala zaman majalisar a ranar Talata, cewa komawar su wata shaida ce ta yancin cin gashin kai. Bello, wanda ya yi magana a madadin sauran takwarorin nasa da aka dakatar, inda ya yaba wa bangaren shari’ar saboda tabbatar da ‘yancinsu da kuma tabbatar da adalci dangane da dakatarwar da akai musu. Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito da cewa, 'yan majalisun da aka dakatar sun shigar da kara a ranar 16 ga Mayu, inda ...