fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Majalisar Wakilai

Majalisa ta nemi Shugaban ‘yansandan Najeriya ya gaggauta yin Bincke kan Rikicin Hausawa da Yarbawa a Sasa

Majalisa ta nemi Shugaban ‘yansandan Najeriya ya gaggauta yin Bincke kan Rikicin Hausawa da Yarbawa a Sasa

Tsaro
Majalisar Wakilai ta nemi Shugaba 'yansandan Najeriya, IGP Muhammad Adamu da ya gunadanar da Bincike cikin hanzari kan rikicin Sasa, Akiyele jihar Oyo.   Majalisar ta bayar da wannan Umarnine a jiya, Litinin   Kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana haka a zaman majalisar inda yace majalisar na aikewa iyalai da gwamnatin jihar Oyo ta'aziyyar wanda suka rasu.   Sannan yayi Alkawarin amfaninda damar majalisar wajan ganin cewa irin hakan bata sake aukuwa ba na gaba.   “Last week, I spoke about the rising spate of insecurity and conflict across the country. Shortly after, and throughout the weekend, the warnings about the dangers we face manifested in Ibadan, the Oyo State of Nigeria where an explosion of violence led to citizens’ death an...
Ka yi Hakuri, Ba dan Mu kunyata ka bane>>Majalisa ta janye gayyatar da tawa shugaba Buhari

Ka yi Hakuri, Ba dan Mu kunyata ka bane>>Majalisa ta janye gayyatar da tawa shugaba Buhari

Siyasa
Majalisar wakilai ta janye gayyatar da tawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa gabanta dan neman baasi kan matsalar tsaro data sha kan Najeriya.   Majalisar ta bayyana cewa gayyatar shugaban kasar ta kawo rarrabuwar kai a siyasance da kuma bangarori na kasarnan, Kamar yanda TheNation ta bayyana.   Hakanan ainahin wanda suka fara maganar gayyatar sun baiwa shugaban kasar Hakuri inda suka bayyana cewa ba dan su kunnyata Shugaban kasar bane. 'Yan majalisar dai sun nemi shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gurfana a gabansu bayan kisan da akawa Manoma da dama a Borno.
Shugaba Buhari ya Zillewa gayyatar Majalisa: Majalisar Wakilai ba ta da ikon gayyatar Shugaba Buhari>>Ministan Shara’a Malami

Shugaba Buhari ya Zillewa gayyatar Majalisa: Majalisar Wakilai ba ta da ikon gayyatar Shugaba Buhari>>Ministan Shara’a Malami

Siyasa
Ministan Shari'a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami ya ce majalisar kasa ba ta da hurumin gayyatar Shugaba Muhammadu Buhari.   Idan za ku iya tuna cewa majalisar wakilai a makon da ya gabata ta zartar da kudurin sammaci ga shugaban kasar kan karuwar matsalar rashin tsaro a kasar. An shirya shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bayyana gaban majalisar dokokin kasar ranar Alhamis amma yanzu ba a tabbatar ko zai mutunta bukatar ba.   A wata sanarwa a ranar Laraba, Malami ya ce baya ga ikon kundin tsarin mulki na majalisar kasa ta gayyaci shugaban kasa kan “amfani da sojojin da yake yi”.
Majalisa na shirin yin dokar da zata hana kotu tsige shugaban kasa da gwamnoni

Majalisa na shirin yin dokar da zata hana kotu tsige shugaban kasa da gwamnoni

Siyasa
Majalisar wakilai na duba wani kudirin doka da dan majalisa, Solomon T. Bob ya samar wanda zai hana kotu tsige shugaban kasa ko gwamna saboda an kama abokin takararsu da takardun bogi.   Kudirin dokar wanda aka gani a jiya, Litinin, kamar yanda Vanguard ta ruwaito ya bayyana cewa kotu ko kuma kotun sauraren karar zabe ba zata cire shugaban kasa ko gwamna ba saboda an sami abokin takararsa da takardun bogi ko wanda basu cancanta ba. Kudirin dokar a yanzu ya bukaci da dan takarar shugaban kasa da ya riga ya ci zabe ko kuma na gwamna idan aka samu irin wannan matsala to ya dauko wani daga cikin jam'iyyar daya tsaya takara a cikinta ya maye mataimakin nasa amma kada ace za'a tsigeshi.   A law to bar courts and election tribunals from voiding the election of a Presi...
Mu ba ‘yan Amshin Shatan Gwamnati bane>>Majalisar Wakilai

Mu ba ‘yan Amshin Shatan Gwamnati bane>>Majalisar Wakilai

Siyasa
Majalisar Wakilai ta karyata zargin da ake mata na cewa 'yar Amshin shatar gwamnati ce.   Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu ne ya bayyana haka bayan dawowar Majalisar Daga Hutun da ta je a yau. Yace ba komai bane da bangaren zartaswa suka aika musu suke amincewa dashi ba sai sun duba sun ga cewa zai amfani 'yan Najeriya.   Ya baiwa 'yan Nakeriya tabbacin cewa majalisar na tare dasu a koda yaushe kuma zata ci gaba da kare Muradunsu.
Majalisa zata gayyaci shugaba Buhari saboda kin amsa gayyatar ta da wasu ma’aikatansa da ake zargi da aikata ba daidaiba

Majalisa zata gayyaci shugaba Buhari saboda kin amsa gayyatar ta da wasu ma’aikatansa da ake zargi da aikata ba daidaiba

Siyasa
Majalisar wakilai ta yo barazanar gayyatar shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya gurfana a gabanta saboda kin amsa gayyatar ta da tawa wasu ma'aikatansa suka yi.   Kwamitin dake kula da Asusun Ajiyar kudin gwamnati na majalisar yace shuwagabannin ma'aikatun CBN, NNPC, NPA sun ki amsa gayyatar da ta musu. Yace akwai wasu harkar kudi ne da ba'a yi bisa ka'ida ba da kuma wasu ayyukan da na wasu ma'aikatun da wadanan hukumomi zasu amsa tambaya akai.   Shugaban Kwamitin,  Wole Oke ya bayyana bacin ransa kan kin amsa gayyatar da wadannan shuwagabannin ma'aikatu suka yi inda yace a aikewa shugaba a sanar dashi hakan dan ya tursasawa wadannan shuwagabannin ma'aikatu su girfana a gaban makalisar.
Kuma Dai: Majalisa ta gayyaci kamfanin mai na kasa, NNPC kan Zargin Biliyan 13

Kuma Dai: Majalisa ta gayyaci kamfanin mai na kasa, NNPC kan Zargin Biliyan 13

Siyasa
Majalisar Wakilai ta gayyaci kamfanin mai na kasa, NNPC da wasu karin Kamfanonin mai kan zargin kin biyan kudin kwangila da aka musu da kuma Almundahanar wasu kudade.   Majalisar ta bukaci kamfanonin su bayyana a gabanta nan da 12 ga watan Agusta dan yin bayani. Kamfanin DE COON Services Limited ne ya aikewa da majalisa Bukatar Binciken inda ya zargi kamfanonin da wannan Almundahana.
Majalisa ta sake gayyatar shugaban NDDC da ya suma a gabanta

Majalisa ta sake gayyatar shugaban NDDC da ya suma a gabanta

Siyasa
Majalisar tarayya ta bayyana cewa, duka tsaffin shuwagabannin hukumar kula da yankin Naija Delta, NDDC na da dana yanzu su bayyana a gabanta dan bayanin yanda Biliyoyin Naira suka bata.   Majalisar ta yi wannan gayyatane ta hannun kwamitin dake kula da asusun ajiyar ma'aikatun gwamnatin tarayya. Kuma wannan gayyata ta dabance da ta farko da kwamitin majalisar dake kula da yankin Naija Delta yayi.   Shugaban kwamitin, Wole Oke ne ya bayyanawa Manema labarai haka inda yace dalilin gayyatar shine saboda yanda idan ana binciken wannan shuwagabanni sai su ce ba'a lokacinsu ne aka yi satar ba shiyasa suke son hada dukkan shuwagabannin a lokaci guda.   Ya kuma jawo hankalin gwamnati cewa kada ta ce zata dauko wasu masu bincike na musamman dan bincikar lamar...
Kuma Dai:Ana zargin Hukumar kula da yakin Arewa maso gabas da batan Naira Biliyan 100

Kuma Dai:Ana zargin Hukumar kula da yakin Arewa maso gabas da batan Naira Biliyan 100

Siyasa
Majalisar wakilai ta fara bincike kan wani zargi na batan Biliyan 100 a ma'aikatar kula da yankin Arewa Maso gabas, NEDC.   A shekarar 2017 ne shugaba Buhari ya samar da wannan ma'aikata inda ta maye tsare-tsaren gwamnatin tarayya na tallafawa yankin. A shwkarar 2019 ne kuma ma'aikatar ta fara aiki. Dan majalisar wakilan, Ndudi Elumelu ne ya fasa wannan kwai inda yace akwai dubban mutane da suka rasa muhallansu da kuma suka shiga tagayyarar rayuwa saboda hare-haren Boko haram, yace dalilin hakane aka kafa wannan ma'aikata dan ta rika kula da kudaden da gwamnatin tarayya da kungiyoyin Agaji masu zaman kansu zasu rika bayarwa na sake ginawa wadanda suka rasa musallansu gidaje da kuma sama musu saukin rayuwa, yace amma kuma hakan bata samu ba.   Yace gwamnatin tar...