fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Makiyaya

Yanzu haka: Makiyaya 4000 ne suka dawo a Jihar Kaduna daga kudu

Yanzu haka: Makiyaya 4000 ne suka dawo a Jihar Kaduna daga kudu

Breaking News
Kimanin makiyaya 4,000 ne suka yi kaura zuwa jihar Kaduna daga kudu sakamakon umarnin da wasu Gwamnonin jihohin suka bayar ga makiyaya masu aikata laifuka da su bar gandun dazukan jihohin. An fadawa manema labarai cewa wani mashahuran makiyaya a jihar, wadanda ke yankin Labduga a karamar Hukumar Kachia, ta fara ganin kwararar wadannan makiyaya da shanunsu, tun makon da ya gabata. Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA) ta tabbatar da faruwar, jami’inta, Hussaini Abdullahi ya ce ya zuwa yanzu sun tabbatar da kimanin 4,000, duk da cewa har yanzu akwai wasu da ke kan hanyar zuwa Kaduna. Abdullahi ya kara da cewa, akasarin makiyayan da suka yi kaura sun rasa abin da za su ci don haka suna bukatar abinci da da agajin gaggawa.
An kashe mutum daya tare da jikkata wasu a yayin arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Yobe

An kashe mutum daya tare da jikkata wasu a yayin arangama tsakanin manoma da makiyaya a Jihar Yobe

Tsaro
Mutum daya ya rasa ransa yayin da da dama suka samu raunuka sakamakon wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a Garin Mallam da ke karamar hukumar Jakusko ta jihar Yobe.   Duk da cewa har yanzu hukumomin ‘yan sanda a jihar ba su tabbatar da faruwar lamarin ba, wani ganau, Musa Amshi, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar.   A cewarsa, “lamarin ya faro ne lokacin da wani bafulatani makiyayi ya kutsa kai cikin gonar da ba a girbe ba.
Kungiyar Miyetti Allah ta hana membobinta sa yara kiwo

Kungiyar Miyetti Allah ta hana membobinta sa yara kiwo

Uncategorized
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta bukaci membobinta da su daina saka yara kiwo a jihar Kaduna.   Sanarwar ta fito ne daga shugaban kungiyar na jihar, Alhaji Musa Haruna Tugga inda ta bayyana cewa an amince da wannan tsari ne dan zaman lafiya da manoma. Yace an dauki wannan matakine dan ganin an daina lalata amfanin gona.   Hakanan kuma kungiyar ta bayyana cewa tana neman hadin kan manoma su bar makiyayan su crika ciyar da shanunsu a guraren kiwo da aka ware.
Da Dumi-Dumi: Mutane uku sun rasa rayukansu yayin wata arangama da akayi tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa

Da Dumi-Dumi: Mutane uku sun rasa rayukansu yayin wata arangama da akayi tsakanin manoma da makiyaya a jihar Jigawa

Tsaro
An bayar da rahoton kashe mutane uku a ranar asabar sakamakon wata arangamar da ta barke tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar, Barkono Jaji-Adiyani wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce ya shaida jana'izar dukkan mamatan. Hakanan, jami’in yada labarai na karamar hukumar, Sunusi Doro, ya kara da cewa fadan ya faru ne a lokacin da wani mazaunin unguwar Arin ya sami rauni yayin da wasu yan fulani suka tare shi a hanyar daji. Ya ce lamarin ya haddasa rikici tsakanin al'ummomin manoma da makiyaya a yanzu. Ya ce dukkan wadanda abin ya shafa mazauna garin Adiyani ne, inda Kanuri suka fi yawa. Jami'in ya bayyana sunan mamatan, Muhammadu Baushe, Maigida Kolo kuma ya ce har yanzu ba a gano sunan mamac...