fbpx
Monday, June 27
Shadow

Tag: malam aminu ibrahim daurawa

HUKUNCIN LAIFIN FYAƊE DAGA MAL AMINU DAURAWA

HUKUNCIN LAIFIN FYAƊE DAGA MAL AMINU DAURAWA

Uncategorized
Ana duba idan ya yi amfani da makami ko karfi, Saboda haka wanda ya yi wa mace fyade ta hanyar amfani da makami hukuncinsu guda da wanda ya yi fashi da makami, ma'ana hukucinsa kisa kai tsaye. Idan ya kasance mace ce mai girma kuma akwai laifinta a wannan bangaren to hukuncin zina ne ya hau kan wanda ya yi fyaden, hukuncin zina kuwa dama idan yana da aure to za a kashe shi, idan kuma bai taba aure ba to za a yi masa bulala 100 da daurin shekara guda da kuma tarar dala dubu 80 (kwatankwacin Naira miliyan 31) kamar yadda aka kayyade a yanzu. Idan karamar yarinya aka yi wa fyade, malamai sun yi fatawar cewa hukuncinsa na kisa ne, idan kuma diyya za a karba to kwatankwacin ta kisa za a karba, domin kuwa ya lalata ta, idan kuwa dama mutum ya lalata wa mace mutuncinta ko ita ta lalatawa na...
HATSARIN BOKAYE DA MATSAFA:Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

HATSARIN BOKAYE DA MATSAFA:Daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Uncategorized
  MANZON ALLAH SAW YACE: DUK WANDA YAJE WAJAN BOKA KO ƊAN TSUBBU (MAI BADA LABARIN ABINDA YA WUCE KO KUMA ABINDA ZAIZO NAN GABA) ALLAH BA ZAI KARƁI SALLAR SA BA TA KWANA 40.   MANZON ALLAH SAW YACE :DUK WANDA YAJE WAJAN BOKA MAI DAAWAR YASAN GAIBU, YA KUMA GASKATA SHI ACIKIN ABINDA YA BASHI LABARI, HAƘIƘA YA KAFURCEWA ABINDA AKA SAUKARWA ANNABI SAW. ABUBUWAN DA SUKE KAI MUTANE WAJAN BOKAYE, NA ƊAYA, NEMAN WANI MAGANI NA WATA CUTA DA TA GAGARA NA BIYU, NEMAN MALLAKAR MIJI KO MATA NA UKU, RABA TSAKANIN MASOYA KO MAAURATA. KO IYAYE NA HUƊU, NEMAN MULKI KO KUƊI. NA BIYAR, KORAR KISHIYA KO HAUKATATA. NA SHIDA, NEMAN MIJI KO KORAR ALJANNU. NA Bakwai, NEMAN A KASHE WANI KO A HAUKATA SHI. 1 BOKA SHINE MAI DAAWAR YASAN GAIBU, KO ƘARYA YA KEYI KO KUMA ...
Ina godiya da Addu’o’in da kuke min:Ina sanar daku cewa ina samun sauki sosai>>Sheikh Daurawa

Ina godiya da Addu’o’in da kuke min:Ina sanar daku cewa ina samun sauki sosai>>Sheikh Daurawa

Uncategorized
Shehin malamin addinin Musulunci,  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya mika godiyarsa ga 'yan uwa da suke sakashi cikin addu'o'in su inda yace yana godiya sosai.   Malamin wanda a baya saboda rashin lafiyar da yayi, wasu suka rika yada cewa ya mutu,amma daga baya ya fito ya karyata, yace yana godiya da addu'a.   Sanarwar ta fitone daga shafin Malam Na facebook inda yace:   "Assalam alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuh, Muna godiya ga yan uwa masu albarka na nesa da na kusa, bisa ga addu'o'i da suke yiwa malam domin samun lafiya. Muna sanar da ku cewa malam yana godiya, kuma yana kara samun sauki da izinin Allah."   Muna fatan Allah ya baiwa Malam Lafiya.
Falalar Watan Sha’aban

Falalar Watan Sha’aban

Uncategorized
WATAN SHA'ABAN wannan wata shine wata na takwas a kalandar musulunci, yana tsakanin Rajab da Ramadan. Asalin sunan wannan wata ya samo asali daga tarwatsewa ko rarrabuwa, domin Larabawa suna tafiya neman ruwa, a cikin watan wata, ko kuma suna yawan kai hare hare ga juna a cikin wannan watan shi yasa aka kira shi da suna Sha'aban, Ibn Hajar Fathul Bari. 4/213.     2. Falalar watan Sha'aban. Usamatu Ɗan Zaidu ya tambayi Manzon Allah saw yace : ya Rasulallah Banga kana yin azumi a cikin wani wata ba kamar yadda ka ke yi a cikin wannan watan? Sai yace wannan wata ne da mutane suke shagala a cikin sa saboda yana tsakanin Rajab da Ramadan, kuma a cikin sa ake ɗaga Aiyukan bayi zuwa sama, don haka nake son a ɗaga aiyuka na ina azumi, Albani ya Hassana shi.   3. Y...

Nasiha daga Malam Aminu Ibrahim Daurawa

Uncategorized
zamo na kowa koda kowa bai zamo naka ba. Yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yima fatan sharri, saka dukkanin musulmi a cikin addu'arka koda babu mai sakaka a cikin addu'arsa. Nufi kowa da alheri koda akwai masu nufanka da sharri. Kyautata tsakaninka da Allah kada kadamu da abinda mutane suke cewa akanka. Allah ya kyautata rayuwarmu Ameen.