fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Tag: Malam Nasiru Ahmad El-Rufai

Gwamna El-Rufai ya fallasa daga inda ‘yan Boko Haram ke samun kudi

Gwamna El-Rufai ya fallasa daga inda ‘yan Boko Haram ke samun kudi

Laifuka, Siyasa
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, Boko Haram na samun kudi daga wajan garkuwa da kutane da harkokin 'yan Bindiga da ake yi a Arewane.   Ya bayyana haka a hirar da aka yi dashi a Channels Tv inda kuma yace 'yan Bindigar sun mayar da hankali kan jihar Kaduna ne saboda cewar da yayi ba zai yi Sulhu dasu ba.   Gwamnan ya kuma tabbatar da matsayarsa ta kin yin Sulhu da 'yan Bindigar indaa yace kisa ne ya dace dasu.
Gwamnatin jihar Kaduna zata daina dogaro da Gwamnatin tarayya>>Gwamna El-Rufai

Gwamnatin jihar Kaduna zata daina dogaro da Gwamnatin tarayya>>Gwamna El-Rufai

Siyasa
Gwamnan jihar Kaduna,  Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatin jihar sa zata daina dogari da kudi daga gwamnatin tarayya.   Ya bayyana hakane a yayin kaddamar da wani zama kan karbar Haraji. Yace jihar ta fadada yanda take karbar Haraji da kuma kasheshi a bangaren Ilimi, Kiwon Lafiya da Raya kasa.   Yace a shekarar 2020, Jihar Kaduna ta samu kudin shiga na kashin kanta da suka kai Biliyan 50.9.   Yace nan gaba, shekaru 4 zuwa 5, gwamnatin jihar zata rika dogaro da kanta ba tare da kudin da gwamnatin tarayya ke bata ba. The governor disclosed that the state’s Internally Generated Revenue (IGR) rose to N50.9 billion in 2020. According to him, the state remains focused on further improving tax collection to reflect its vision. “In ou...
Yanda El-Rufai ya kala min sharri cewa wai nine ke daukar nauyin Boko Haram amma gashi har yanzu akwaita, kuma tana kashe mutane da yawa fiye da lokacin Mulkina>>Goodluck Jonathan

Yanda El-Rufai ya kala min sharri cewa wai nine ke daukar nauyin Boko Haram amma gashi har yanzu akwaita, kuma tana kashe mutane da yawa fiye da lokacin Mulkina>>Goodluck Jonathan

Siyasa
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa a shekarar 2014, Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kala masa sharri shi da tsohon shugaban CAN, Pastor Ayo Oritsejafor cewa sune ke daukar Nauyin Boko Haram.   Yace an zargesu da Daukar nauyin Boko Haram wai dan su rahe yawan mutanen Arewa, da kuma bata sunan Musulunci.   Yace El-Rufai ya wallafa a shafinsa na sada zumunta sannan kuma a Landan ma ya sake yin irin wannan maganar.   Jonathan ya bayyana hakane a cikin littafinsa na My Transition Hour, ya kuma bayyana cewa, yanzu shekaru bayan ya sauka daga Mulki, ga Boko Haram nan ta ci gaba inda ta kashe mutane da yin garkuwa da mutane fiye da lokacinsa. “A particular opposition politician, Nasir El-Rufai, who became the Governor of K...
Yan bindiga ba su isa su sa mu rufe makarantu ba>>El-Rufa’i

Yan bindiga ba su isa su sa mu rufe makarantu ba>>El-Rufa’i

Tsaro
Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya Malam Nasir el-Rufai ya ce hare-haren da 'yan bindiga masu satar mutane domin karbar kudin fansa ke kai wa a jihar a baya-bayan nan na barazana ga sha'anin ilmi. Gawmnan ya ce sabanin wasu jihohin arewacin da ke fama da matsalar tsaro wadanda suka rufe makarantu saboda fargabar hare-hare, jihar Kaduna ba za ta rufe nata makarantun ba. Har yanzu 'yan bindiga ba su sako akalla dalibai talatin da tara na wata kwaleji da kuma malaman wata makarantar firamare uku da suka sace a baya-bayan nan ba. Bayan wani babban taron masu ruwa da tsaki kan tsaro a jihar jiya, gwammna El-Rufai ya shaida wa abokin aikinmu Yusuf Tijjani cewa gwamnatin jihar na kan bakanta na cewa ba zata yi sulhu ko ta rika biyan kudin fansa ga 'yan bindiga ba. BBChausa.
Duk da hare-haren ‘yan Bindiga dake karuwa, Gwamna El-Rufai ya nanata cewa ba zai yi Sulhu dasu ba

Duk da hare-haren ‘yan Bindiga dake karuwa, Gwamna El-Rufai ya nanata cewa ba zai yi Sulhu dasu ba

Tsaro
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, yana nan kan bakansa na cewa ba zasu yi sulhu da 'yan Bindiga ba.   Ya ce amma daidaikun mutane, kamar malaman addinai zasu iya yi. Hakan na zuwane bayan da 'yan Bindigar suka sace dalibai 39 a makarantar tarayya dake Afaka a jihar.   Gwamnan yace suma suna so 'yan Bindigar su tuba amma ba sune zasu je suna rokonsu su tuba ba.   “We will not engage with bandits or kidnappers. Private citizens like clerics and clergymen can do so in their individual capacities, to preach to them and ask them to repent.   “We also want them to repent but it is not our job to ask them to do so,’’ he said.
Banji ciwon komai ba da aka min rigakafin Coronavirus/COVID-19>>Gwamnan Kaduna

Banji ciwon komai ba da aka min rigakafin Coronavirus/COVID-19>>Gwamnan Kaduna

Kiwon Lafiya
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa bai ji ciwon komai ba da aka masa Rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19.   A jiyane dai akawa Gwamnan da mataimakiyarsa, Hadiza Balarabe rigakafin cutar.   Da yake bayyana yanda yaji bayan rigakafin ta shafinsa na sada zumunta, Gwamna El-Rufai yace bai ji ciwon kai ko wani avu ba da aka masa rigakafin,  kuma ya ci abinci. Ya bayyana cewa rigakafin bashi da Illa. He wrote: “Astrazeneca vaccine is safe: Just had my first meal some 5 hours after taking my first dose of the Oxford-AstraZeneca vaccine. No pain. No headache. No side effects. Excellent appetite.”
Gwamna El-Rufai ya baiwa tsohon Sarkin Kano, Sanusi II mukami a hukumar KADIPA ta Jihar Kaduna

Gwamna El-Rufai ya baiwa tsohon Sarkin Kano, Sanusi II mukami a hukumar KADIPA ta Jihar Kaduna

Siyasa, Uncategorized
Gwamna Nasir El-Rufai ya nada tsohon Sarkin Masarautar Kano, Mohammed Sanusi, a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar Raya Jarin Kasuwancin Kaduna (KADIPA). El-Rufai ya kuma umarci hukumar da ta ninka kokarin ta na sanya jihar a sahun gaba a duk fadin Najeriya, ta hanyar inganta matsayin saukaka harkokin kasuwanci. El-Rufai, wanda yayi magana a wajen bikin kaddamar da hukumar, ya yiwa Sanusi II maraba a hukumance. Ya kuma godewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, bisa karban hidimtawa mutanen jihar Kaduna. El-Rufa'i ya ce hukumar ta kasance muhimmiyar hanya kuma mai nasara a harkar saka jari a Kaduna, kuma ta fitar da sama da dala biliyan 2.1 a zahiri. El Rufa'i ya ci gaba da cewa KADIPA za ta yi takara ba kawai tare da sauran jihohin Nijeriya don saka hannun...
Jihar Legas ta yi sa’ar samun Gwamnoni masu son ci gaba>>Gwamna El-Rufai

Jihar Legas ta yi sa’ar samun Gwamnoni masu son ci gaba>>Gwamna El-Rufai

Siyasa
Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa jihar Legas ta yi sa'ar samun Gwamnoni masu son ci gaba.   Ya bayyana hakane a ganawar da aka yi dashi a wani taron tattalin arziki da ya gudana A Jihar. Gwamnan yace Legas da kasa ce to zata zama itace kan gaba a kasashen Africa wajan tattalin arziki.   Yace ci gaban Legas na damfare da ci gaban Najeriya.  Gwamna El-Rufai yace jiharsa ta Kaduna na kwaikwayon Legas inda yace Legas din ce ta fara canja tsarin haraji kuma itama Kaduna ta bi sahunta.   Ya bayyana cewa zaau ci gaba da goyon bayan ci gaban jihar ta Legas.   “If Lagos were a country, it would have a bigger GDP than many African countries. For us in Kaduna state, Lagos is a model that we follow. You started the tax reform...
Yan Bindigar da suka gana da Sheikh Gumi sunce zasu yi maganin Gwamna El-Rufai

Yan Bindigar da suka gana da Sheikh Gumi sunce zasu yi maganin Gwamna El-Rufai

Siyasa
Yan Bindigar dake tada kayar baya a Tegina dake Jihar Naija da kuma Birnin Gwari a jihar Kaduna sun sha Alwashin maganin Gwamna Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai.   Yan Bindigar sun bayyana hakane a yayin ganawa da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ranar Alhamis a dajin Tegina.   A baya dai gwamna El-Rufai ya nemi a kashe 'yan Bindigar saboda yace ba zasu daina ba sanna kuma yaki amincewa da magamar sulhu ko kuma yi musu Afuwa.   Wata Majiyar Tsaro a wajan ganawar da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi da Dogo Gide ta bayyana cewa yayi Alwashin ci gaba da kai hare-hare a jihar Kaduna kuma babu abinda zai faru.   Yace su basa tsoron Mutuwa. Saidai Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya rokesu da su yi hakuri saboda duka gwamnonin Arewa sun amince a yi sulhu. He told the de...
Hanya daya ce kawai matasa zasu iya kwace Mulki daga hannun tsaffi irina>>Gwamna El-Rufai

Hanya daya ce kawai matasa zasu iya kwace Mulki daga hannun tsaffi irina>>Gwamna El-Rufai

Uncategorized
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa ya kamata kwararrun mutane su rika shiga siyasa.   Yace sai an shiga siyasa ne sannan za'a iya kawo canjin da ake nema. El-Rufai ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a Legas.   Ya bayyana cewa, kada kwararru su rika zuwa suna aiki da kamfanoni masu zaman kansu, abinda ya kamata shine su rika shiga siyasa ana damawa dasu.   Yace zanga-zanga babu inda zata kai mutum, abinda ya kamata shine ya shiga siyasar ayi dashi.