
Tsohon shugaban kasar Mali, Amadou Toumani Toure ya rasu
Tsohon Shugaban Mali Amadou Toumani Touré ya rasu yana da shekara 72.
Ya mutu ne da safiyar yau Talata a Turkiyya, inda likitoci ke kula da shi bayan ya isa birnin Istambul a 'yan kwanaki da suka gabata.
Kafin ya bar Mali, an yi masa tiyatar gaggawa a zuciya a wani asibiti da ke babban birnin ƙasar, Bamako.
Ya shugabanci Mali daga 2002 har zuwa sanda aka tumɓuke shi a juyin mulkin sojoji a 2012, wanda Janar Amadou Haya Sanogo ya jagoranta.
An yabi Mista Touré game da kawo ƙarshen mulkin sojoji na tsawon shekaru tare da miƙa shi ga farar hula ta hanyar shirya zaɓe a 1992.
Ana yi masa laƙabi da "sojan dimokuraɗiyya".
Mali's former president, Amadou Toumani Touré, has died at the age of 72, a family member and a doctor said on Tuesday November 10.
"Amadou Toumani Toure di...