fbpx
Wednesday, July 6
Shadow

Tag: mamaki

Kare na samun kulawar da mutane basa samu

Kare na samun kulawar da mutane basa samu

Uncategorized
A kasar Amurka, karnuka na samun irin kulawar da wasu mutanen basa samunta, anyi kiyasin cewa a shekarar data gabata, masu son da kiwon dabbobin gida, irin su mage da kare dadai sauransu sun kashe zunzurutun kudi dalar Amurka biliyan shida wajen kula dasu.  Akwai guraren da ake kai karnukan dansu shakata, kuma a kula dasu yanda ya kamata, akwai wani hotal din karnukan da ake kai kare dan gata ya kwana cikin annashuwa, za'amai yankan farcensi, a gogesu a sakamusu wani mai da zaisa su rika sheki, akwai gurin ninkaya/wanka na musamman a gurin, haka kuma ana wankemusu  hakoransu, a musu tausa. Idan aka kai kare daki, ya kasa yin barci, akwai ma'aikacin hotal din da aka ware na musamman da zai je ya debemishi kewa har ya kamu da barci ko kumama sai gari ya waye, haka kuma akwai...
An kama kasurgumar barauniya me shekaru tamanin da shida da satar gwal

An kama kasurgumar barauniya me shekaru tamanin da shida da satar gwal

Uncategorized
Doris Payne 'yar shekaru tamanin da shida wata kasurgumar barauniyar gwalagwalaice wadda satarta bata tsaya a kasar Amurka inda aka haifeta kadaiba, harma wasu kasashe take ketarawa domin dai kawai ta saci sarka, dankunne, ko abin hannun gwal. Ta shafe shekaru 65 tana wannan harkar sata wadda takai har ana kiranda ta sunan me sana'ar sata. Tana kyankyara kwalliyane Yanda idan ka ganta bazaka taba cewa bata da kudiba, sai ta shiga shagon sayar da gwalagwalai ta kira a kawomata kala-kalar gwal tana dubawa, a haka zataja me sayar da gwaldin da hira har ya manta yawan gwalagwalan daya kawomata sai ta shammaceshi ta dauki wanda take so ta fiyarta. A tarihin sace-sacen da Doris tayi, an kamata da satar gwal har sau bakwai, akwai lokacin da tayi wata babbar sata wadda tafi kowacce na gwal wa...

A kasar yurugai shan tabar wiwi ba laifi bane

Uncategorized
Uruguay ta zama kasa ta farko a duniya da ke nomawa da sayar da tabar wiwi a dokance don nishadi. Tun da farkon safiyar Laraba ne mutane suka kafa layuka a gaban kantunan sayar da magunguna guda 16 da ke da izinin sayar da wiwi. Kuma da tsakar rana ne tabar ta kare a akalla daya daga ciki kantunan. Don hana wiwin shiga hannun masu yawon shakatawa, 'yan kasar Uruaguay ne kadai da suka haura shekara 18 ka iya yin rijista don saye. Ta hanyar amfani da shaidar zanen yatsu, mutum na iya sayen sama da gram 40 duk wata don yin bushi. Ana sayar da nau'i biyu na tabar ta wiwi, duka na kunshe da sinadarin THC (tetrahydrocannabinol) wani kwakkwaran mahadi da ke sa kai ya yi caji. Manufar wannan sauyi ita ce rage fataucin tabar. Masu aikowa BBC rahotanni sun ce kasashen Latin Amurka na k...
Ya kashe Diyarshi Saboda tanaso ta auri musulmi

Ya kashe Diyarshi Saboda tanaso ta auri musulmi

Uncategorized
Wani mutum dan kasar Isra'ila ya kashe diyarshi ta hanyar caka mata wuka saboda ta nace sai ta auri saurayinta musulmi. Mahaifinnata wanda shi ba musulmi bane yayi kokarin rabata da saurayin nata amma yarinyar fur taki yarda, tace ita tana son shi. Saurayin nata yana kulle a gidan yari kuma tayi alkawarin zata musulunta idan ya fito daga gidan yarin yanda daga karshe sai suyi aure, hakan ya kara hasala babanta me suna Sami, ya rika mata dukan rashin imani, kamar jaka, dataga abin nashi ba wanda zata iya jurewa bane, saita gudu ta tafi gidan mahaifiyar saurayinta ta zauna acan. Yarinyar ta rika kiran kawayenta tana gayamusu cewa mahaifinta na kokarin kasheta, abin yana bata mamaki. Mahaifin nata ya kasa jurewa ya bita can gidan mahaifiyar saurayin nata ya dawo da ita gida, daga nann...