
Ba’a Fahimci Mamman Daura bane>>Shugaba Buhari ya kare dan uwansa
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya bayyana cewa da yawa basu fahimci dan uwansa Mamman Daura ba.
Ya bayyana hakane a sakon taya murnar cika shekaru 81 da ya aikewa mamman Daura ta bakin kakakinsa, Malam Garba Shehu.
Shugaba Buhari yace Mamman Daura Mutum ne me matukar Hakuri sannan jajirtacce ne wanda yayi aiki dan bautawa Najeriya da ma Duniya baki daya.
Shugaba Buhari yace Mamman Daura mutum ne wanda ya kware a fannin aikinsa da kuma fannonin Rayuwa wanda da wuya ku zauna tare ba da ka amfana da wani abu daga gareshi ba.
Shugaban ya taya Mamman Daura murnar zagayowar ranar haihuwarsa inda yace yana mai fatan tsawon rai da kuma lafiya.