fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Tag: Manchester United

Arsenal 0-0 Manchester United: A karin farko United ta buga wasanni 18 wanda bana gida ba a jere ba da shan kashi ba

Arsenal 0-0 Manchester United: A karin farko United ta buga wasanni 18 wanda bana gida ba a jere ba da shan kashi ba

Wasanni
Burin Manchester United na lashe kofin Premier League ya kara ja baya yayin da ta raba maki da Arsenal inda suka tashi wasa babu ci, bayan data fadi wasa tsakanin tada Southampton daci 2-1. Duk da haka dai United ta kasance ta biyu a saman teburin Premier League, kuma tayi nasarar kafa sabon tarihi inda yanzu ta buga wasanni 18 na Premier League wanda bana gida ba a jere ba tare da tasha kashi ba. Arsenal wadda ta kasance ta 8 a teburin Premier League din ta kusa cin kwallon a wasan bayan da Xhaka ya bugi sandar raga a harin daya kai, sannan kuma sakamakon wasan yasa yanzu ta buga wasanni 7 a jere ba tare da shan kashi ba a wannan kakar. Manchester United set new record after goaless draw with Arsenal Manchester United set a new club record of 18 league away games without defea...
Manchester United 1-2 Sheffield United: A karin farko Sheffied tayi nasarar doke Manchester a gidanta tun shekara ta 1973

Manchester United 1-2 Sheffield United: A karin farko Sheffied tayi nasarar doke Manchester a gidanta tun shekara ta 1973

Wasanni
Kungiyar Sheffield United tayi nasarar lallasa Manchester United a filin tana Old Trafford karo na farko tun shekara ta 1973, wanda haka  yasa ta kawo karshen wasanni 8 daga buga tana shan kashe a hannun United. Kungiyar Sheffield ta ci kwallayen ne ta hannun Kean Bryan da kuma Olivier Burke wanda duk suka kasance kwallayen su na farko a a gasar Premier League, yayin da Manchester kuma taci kwallo ta hannun Maguire. Bryan da Burke sun zamo yan wasa guda biyu na farko da suka yi nasarar cin kwallayen su na farko a Premier League tsakanin su da United, tun bayan da Jamie Verdy da Cambiaso suka yi hakan a kungiyar Leicester shekara 2014. Sakamakon wasan yasa Manchester United ta rasa damar darewa saman teburin Premier League inda ta kasance ta biyu da maki 40. Manchester United 1-2 Shef...
Mawuyacin abune ganin babban mafarkina yazo karshe>> Odion Ighalo

Mawuyacin abune ganin babban mafarkina yazo karshe>> Odion Ighalo

Wasanni
Kantirakin aron tauraron dan wasan Najeriya a kungiyar Manchesrer United, Odion Ighalo zai kare ne a karshen wannan watan inda zai koma kungiyar shi ta kasar Sin Shanghai Shenhua amma duk haka yana fatan United zata lashe Premier League da kofin FA a wannan kakar. Ighalo yayi nasarar zira kwallaye biyar a wasanni 23 daya bugawa Manchester United tunda ya koma kungiyar a rana ta karshe da za'a kulle kasuwar yan wasan watan janairu ta kakar bara, amma wasanni biyu kacal ya fara bugawa Manchester a wannan kakar tun bayan da suka siya Edinson Cavani. Ighalo ya bayyana cewa "Mawuyacin abune gamin babban mafarkina yazo karshe, amma ina godiya ga Allah wanda shine ya cika min burina na taka leda a mashahuriyar kungiya Manchester United." Dan wasan wanda ya buga mintina 9 a wannan kakar y...
Manchester United na shirin siyar da Marcus Rojo da Jesse Lingard

Manchester United na shirin siyar da Marcus Rojo da Jesse Lingard

Wasanni
Gwanin kasuwar kwallon lafa, Fabrizio Romano ya ruwaito cewa kungiyar Manchester United na shirin siyar da yan wasan ta guda biyu, Marcos Rojo da kuma Jesse Lingard nan da wasu yan kwanki. Marcua Rojo na shirin komawa kungiyar Boca Junior ne dake kasar Argentina yayin da shi kuma Jesse Lingard zai tafi izuwa kungiyar West Ham ta gasar Premier League a matsayin aro. Manchester United na kokari sosai a wannan kakar, yayin da take jagoranci da maki biyu a saman teburin gasar Premier League kuma ta cire Liverpool daci 3-2 a gasar kofin FA. Manchester United are set to let Rojo and Lingard go in the coming days. Manchester United are now open to let Jesse Lingard and Marcos Rojo go in the next days, according to transfer expert Fabrizio Romano. Rojo is waiting for Boca Juniors an...
‘Yan wasan gaba na Manchester United basu kai kwarewar Cavani ba>>Pogba

‘Yan wasan gaba na Manchester United basu kai kwarewar Cavani ba>>Pogba

Uncategorized
Mashahurin dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa dake taka leda a kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya bayyana cewa yan wasan gaba na tawagar United basu kai matakin Edinson Cavani ba. Pogba ya fadi wannan maganar ne bayan da shi da Cavani suka yi nasarar ciwa Manchester kwallaye biyu a wasan data doke Fulham daci 2-1 a daren jiya, inda ta dare saman teburin gasar Premier League. Ana sa ran cewa Edinson Cavani zai dan ringa taimakawa ne kawai ga yan wasan gaba na United masu karancin shekaru, amma sai dai dan wasan ya jajirce sosai inda ya bayyana cewa shima fa yana daga cikin manyan yan wasa a kungiyar. Manchestee United Strikers are not at the same level as Edinson Cavani>>Pogba Paul Pogba has claimed Man Utd's strikers do not possess the same quality as veteran ...
Fulham 1-2 Manchester United: Pogba ya taimakawa Manchester United ta dare saman teburin gasar Premier League

Fulham 1-2 Manchester United: Pogba ya taimakawa Manchester United ta dare saman teburin gasar Premier League

Wasanni
Tauraron dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa, Paul Pogba ya taimakawa Manchester United ta koma saman teburin gasar Premier League inda ta kwace jagorancin gasar a hannun abokan takarar ts Manchester City, wadda ta dare saman teburin bayan data doke Aston Villa daci 2-0. Kungiyar Fulham ce ta fara jagorancin wasan cikin mintina 5 ta hannun Ademola Lookman, kafin Edinson Cavani ya ramawa Manchester United kwallon wadda ta kasance kwallon shi ta hudu kenan a wasannin daba na gida ba a wannan kakar. Bayan Pogba ya kara ciwa United kwallo a wasan, kungiyar Fulham ta kara damara sosai amma sai dai ta kasa ramawa, yayin da ita kuma manchester United ta sake kafa irin tarihinta na samu nasara a wasanni 17 a jere wanda bana gida ba, wanda ta taba kafawa a shekara ta 1999 sannan kuma yanz...
Murza leda a kungiyar Manchester United ba karamin aiki bane>>Pogba

Murza leda a kungiyar Manchester United ba karamin aiki bane>>Pogba

Wasanni
Tauraron dan wasan tsakiya na kasar Faransa, Paul Pogba ya bayyana cewa bugawa Manchester United wasa ba karamin aiki bane bayan da Manchester City ta lallasa a wasan daci biyu a wasan kusa da karshe na gasar kofin EFL. Nasarar da Manchester City tayi a wasan tasa yanzu zata kara da kungiyar Tottenham a wasan karshe na gasar, yayin da Spurs take neman lashe kofi karo na farko a cikin kusan shekaru goma da suka gabata. Bayan an tashi wasan Manchester City da United, Paul Pogba  ya bayyanawa MUTV cewa yanzu basu da lokaci sosai na jin kunya a wannan makon saboda suna mataki mai kyau a gasar Premier League. Kuma wasan su da City ya koya masu darasi sannan kuma zasu kara jajircewa. Dan wasan ya kara da cewa, harkar tamola da kuma murza leda a kungiyar Manchester United ba karamin aiki...
Jadon Sancho ya shirya komawa kungiyar Manchester United>>shugaban Dortmund

Jadon Sancho ya shirya komawa kungiyar Manchester United>>shugaban Dortmund

Wasanni
Tauraron dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Dortmund, Jadon Sancho yayi nasarar cin kwallon shi ta farko a wannan kakar bayan Akanji ya fara zira kwallo a wasan su da Wolfsburg wanda hakan yasa Dortmund ta koma ta hudu a saman teburin gasar Bundlesliga. Jadon Sancho ya kasance babban dan wasan da kungiyar Manchester tayi kokarin siya a kakar bara, amma sai dai ta kasa biyan farashin da kungiyar Dortmund ta sawa tauraron dan wasan nata. Amma yanzu an samu labari daga gwanin kasuwar kwallon kafa, Fabrozio Romano na cewa shugaban kungiyar Dortmund Watzke ya bayyana Jadon Sancho ya shirya komawa kungiyar Manchester United. Romano ya kara da cewa dan wasan ba zai bar Dortmund a wannan kasuwar ta watan janairu ba, amma a karshen wannan kakar ne kungiyoyin tamola zasu fafata wurin siyan ...
Manchester United 2-1: Yayin da Anthony Martial ya kwashe tsawon kwanakin wannan makon yana ciwa Manchester United kwallaye

Manchester United 2-1: Yayin da Anthony Martial ya kwashe tsawon kwanakin wannan makon yana ciwa Manchester United kwallaye

Wasanni
Alamu na nuna cewa kungiyar Manchester United ta shirya fafatawa wurin lashe kofin Premier League bayan da kungiyar ta lallasa Aston Villa daci biyu wanda hakan yasa yanzu makinta ya daidaita dana Liverpool a saman teburin gasar. Antony Martial ne ya taimakawa tawagar Ole Gunnar ta fara jagorancin wasan a minti na 40, yayin da kwallon tasa yanzu dan wasan Ingilan ya zamo dan wasan United na farko daya kwashe gabadaya kwanaki bakwai na mako yana ciwa Manchester kwallaye tun bayan Ryan Giggs,Andrew Cole,Becham da Rooney sunyi hakan. Aston Villa tayi nasarar rama kwallon a minti na 58 ta hannun Traore, amma tauraron dan wasan Manchester Bruno Fernandez yayi nasarar ciwa kungiyar tashi bugun daga kai sai gola wanda hakan tasa aka tashi wasan United na cin 2-1. Wasan ya kasance n...
Ba zamu fara maganar lashe kofi a yanzu ba>>Manajan United bayan ya lallasa Wolves 1-0

Ba zamu fara maganar lashe kofi a yanzu ba>>Manajan United bayan ya lallasa Wolves 1-0

Wasanni
Tauraron dan wasan Ingila,Marcus Rashford yayi nasarar ciwa Manchester United da kwallo guda ana daf da tashi wasa wadda tasa Ole Gunnar ya lashe gabadaya makin wasan kuma tawagar shi ta koma ta biyu a saman teburin Premier League. Sakamakon wasa yanzu United ta buga wasanni tara kenan ba tare da tasha kashi ba amma duk da haka manajan kungiyar Ole Gunnar ya bayyana cewa ba zasu fara maganar lashe kofi a yanzu ba, amma suna da yakinin cewa zasu iya doke duk wata kungiya da zasu kara da ita a yanzu. Bruno Fernandez ne yayi nasarar taimakawa Marcus Rashford ya ciwa Mancheater kwallo guda amma duk da hakan manajan kungiyar ya bayyana cewa Fernandez bai jajirce sosai ba a wasan kamar yadda ya saba.