
Musa ‘Yar adua: Mahaifina yana matuƙar son cin ƙosai da biredi
Tsohon shugaban Najeriya marigayi Umar Musa 'Yar Adua yana matukar sha'awar cin kosai da kuma biredi da miya, a cewar dansa, Musa Yar Adua.
Musa ya bayyana haka ne a tattaunawa ta musamman ta shafin Instagram da Sashen Hausa na BBC kai-tsaye ranar Talata da almuru.
"Mahaifina yana son kosai amma da sanyi, kuma sai can tsakar dare, sannan yana son biredi da miya. Shi mutum ne wanda tsakani da Allah yana da saukin kai. Ko a cikin gidanmu gaskiya ba wanda ya biyo wannan hali ta wannan fannin...zai dawo daga aiki ya ci kosai hankalinsa ya kwanta', in ji Musa Yar Adua.
Ya kara da cewa yana matukar farin ciki game da yadda 'yan Najeriya suke yaba wa mahaifinsa saboda ayyukan da ya yi wa kasar, yana mai cewa "hakan na nufin duk abin da mutum zai yi ya ...