
Brescia sun kori Mario Balotelli saboda haka a kyauta zai koma duk kungiyar daya daidaita dasu
Mario Balotelli ya samu matsala da shuwagaban kungiyar shi ta Brescia saboda bai hallaci wasu gwaje-gwajen da aka yiwa yan kungiyar ba kuma ya jera kwanaki goma baya zuwa atisayi.
Yanzu kuma Republlica sun bayyana cewa rashin biyayyar da dan wasan yayi tasa sun kore shi daga kungiyar su kuma yanzu a kyauta zai koma duk kungiyar daya daidaita dasu saboda baida wani kwantiraki akan shi. Shugaban Brescia ya bayyana cewa siyan Balotelli kuskure ne.
Balotelli ya shiga kungiyar Brescia ne a watan augusta na shekara data gabata kuma wasanni 19 ya buga yayin da yayi nasarar jefa kwallaye guda biyar. Dan wasan mai shekaru 29 ya turawa kungiyar wata takaddar asibiti wadda take nuna cewa yana fama da ciwon ciki sai yasa bai hallaci atisayin ba.