
Hira ta Musamman: Mijin tsohuwar tauraruwar fim, Malika yace Aurensu be mutu ba
A makon da ya gabata ne muka samo muku labarin kishin-kishin din mutuwar Auren tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Muhammad wadda aka fi sani da Maryam Malika daga wata kafa.
Saidai a wata hira da mijin Maryam din, Ukar Muhammad yayi damu ta waya ya tabbatar mana da cewa har yanzu aurensu bai mutu na. Hutudole ya tattaro muku cewa, Umar cikin fushi yace " dan kawai ta hau Instagram shine za'a ce aurenta ya mutu"
Ya kara da cewa "bidiyo ne ta saka kuma ba tsirara take ba, ina yin Instagram naga cewa itama ya dace in mata adalci in barta ta yi shiyasa" kamar yanda ya fada.
Ya kara da cewa an dade ana wannan tsegumi amma abinda yake so a sani shine karyane.
Saurari hirar a kasa: