fbpx
Friday, July 1
Shadow

Tag: Masallaci

Kungiyar Izala Ta Kaddamar Da Sabon Masallaci A Jihar Adamawa

Kungiyar Izala Ta Kaddamar Da Sabon Masallaci A Jihar Adamawa

Uncategorized
Kungiyar IZALA reshen jihar Adamawa ta kaddamar da sabon masallaci wanda wasu bayin Allah daga kasar Qatar suka gina a filin Kungiyar dake unguwar Jambutu a Jimeta-Yola, kuma suka damka masallacin ga kungiyar. Masallacin wanda ya kunshi rijiyan burtsatsai (borehole) da wurin alwala na zamani da bandaki, zai kasance na Juma'a ne. Shugaban Kungiyar IZALA na jihar Adamawa Alh Abubakar Sahabo Magaji ne ya jagoranci kaddamar da masallacin yayin da shugaban majalisar malamai Imam Salihu Umar ya gabatar da nasiha da addu'o'i.
Hoto:Kalli yanda aka rataye kan alade a kofar Masallaci

Hoto:Kalli yanda aka rataye kan alade a kofar Masallaci

Uncategorized
An sanar da cewa wasu masu neman tada zaune tsaye sun rataye kan alade a kofar Masallacin Vaihingen Enz dake karklashin garin Stuttgart a kasar Jamus.     Tarayyar Hadin Kan Turkawa Musulmi (DİTİB) ta sanar da cewa kamarar tsaro ta dauki bidiyon wasu mutum biyu a yayinda suke rataye kan alade a kofar Masallacin Fatih da misalin karfe 23.30 suka kuma ari na kare bayan yin haka.     Shugaban Masallacin Fati mallakar Hukumar DIBIT dake Vaihingen Enz Latif Pekmezci ya bayyana cewar maharan sun zo ne da wata karamar motar bas mallakar wata kanfani kuma an sanarda 'yan sanda game da lamarin.     Pekmezci, wanda ya bayyana matukar bakin cikin afkuwar lamarin ya kara da cewa 'yan sanda sun fara bincike akan lamarin. TRThausa.