fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Tag: Masarautar Zazzau

Da Dumi-Dumi: Ba gaskiya bane cewa zamu bi sahun kano wajan kacaccala masarautar Zazzau>>Mahukuntan Kaduna

Da Dumi-Dumi: Ba gaskiya bane cewa zamu bi sahun kano wajan kacaccala masarautar Zazzau>>Mahukuntan Kaduna

Siyasa
Jinkiri da mahukunta suke yi wurin nadin sabon sarkin Zazzau na ci gaba da jawo cece-kuce da kuma yada labarai mabanbanta game da masarautar, ciki har da maganar rarraba masarautar zuwa gida uku. Tun yammacin ranar Lahadin da aka sa za a bayyana sunan sabon sarkin Zazzau ne dai wasu su ka fara yada labarin cewa gwamnati na niyar raba masarautar yi shi yasa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba.   Bayanin gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i a wajen gabatar da kasafin kudi na badi gaban majalisa, ya kara karfafa jita-jitar raba masarautar saboda kudurin da gwamnan ya ce zai kawowa 'yan majalisa don yin kwaskwarima ga masarautun jahar Kaduna. Sai dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya musanta wannan rade-radi. ...