
Hotunan Ziyarar Sabon Sarkin Zazzau Fadar Gwamnatin Borno
Mataimakin gwamnan jihar Borno Umar Kadafur ya karbi bakuncin Mai martaba Sarkin Zazzau H.R.H Alhaji Ahmed Nuhu Bamali a fadar gwamnatin jihar dake Maiduguri.
Sarkin wanda ya samu rakiyar Galadiman Zazzau Alh. Nuhu Yahaya, Sarkin Fadan Zazzau Alh. Ahmadu Patuka, Dan Madamin Zazzau Alh. Kabir Ibrahim, Sarkin Dawakin Zazzau Alh. Ibrahim Shehu Idris da sauransu.