fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Masari katsina

‘Ban san wanda zai gaje ni ba a matsayin gwamnan jihar Katsina -Inji Gwamna Masari

‘Ban san wanda zai gaje ni ba a matsayin gwamnan jihar Katsina -Inji Gwamna Masari

Siyasa
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya baiyana cewa shi ba shi da kokwanto ko ra'ayi a kan wa zai gaje shi bayan ya sauka daga mukaminsa a shekara ta 2023. Masari wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta musamman da yayi da jaridar The Nation a gidan gwamnati da ke jihar Katsina, Inda ya ci gaba da bayyana sha'awar sa da cewa yana fatan jihar ta samu gwamna da ya fishi a shekara ta 2023, bayan ya kammala wa'adin mulkinsa. Ya ce: '' Da farko dai ban san wanda zai gaje ni ba, kuma abu na biyu shi ne fata na ga jihar Katsina, ta samu gwamna mai inganci sama dani, burina da fatana a samu wanda zai zo bayan ni ya zama ingantaccan jagora. Inji shi Haka zalika ya kara da cewa "Na kasance a cikin Majalisar Dokoki ta kasa kuma a yanzu haka ba ni da niyyar sake  komawa Majalisa...