
Mason Mount ya zamo dan wasa na biyu mafi karancin shekaru bayan Arjen Robben daya ciwa Chelsea kwallaye 10 a Premier League, yayin da Chelsea ta lallasa Sheffield United daci 2-1
Chelsea tayi nasarar fara jagorancin wasan ta hannun Mason Mount kafin Rudiger yayi kuskuren cin gida inda ya ramawa United kwallon, amma bayan mintina hudu Jorginho ya ciwa Chelsea kwallo ta biyu da bugun daga kai sai me tsaron raga.
Mason Mount dan shekara 22 yayi nasarar zama dan wasa na biyu mafi karancin shekaru bayan daya ciwa Chelsea kwallaye 10 a gasar Premier League, bayan Arjen Robben wanda yayi hakan yana dan shekara 21.
Kwallo guda kacal aka zira a ragar Chelsea a wasanni hudu da Thomas Tuchel ya ya fara jagoranta, wanda hakan ya kasance karo na farko tun bayan Guus Hiddick a shekara ta 2009.
Hutudole ya samo cewa, Sakamakon wasan yasa Chelsea ta koma ta biyar a teburin gasar Premier League kuma tazarar maki guda ne kacal tsakanin tada Liverpool wadda tasha kash...