
An yi garkuwa da mutane 10 a jihar Kaduna a gonakinsu
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa mutane 10 ne a jiya, Asabar masu garkuwa da mutane suka sace a jihar.
Mutanen sun je gonakinsu ne dake Kauyen Kuriga a karamar hukumar Chukun dake jihar yayin da wannan ibtila'i ya Afka musu. Hutudole ya fahimci har yanzu wadannan mutane suna hannun wanda suka yi garkuwa dasu din.
Sanata Shehu Sanine ya tabbatar da wannan labari ta shafinsa na sada zumunta.
https://twitter.com/ShehuSani/status/1297530424152010754?s=19
Yayi kira ga mahukuntan jihar da su dauki matakin da ya dace dan ganin an kubutar da wadannan mutane.