fbpx
Thursday, June 30
Shadow

Tag: Matasa

Ku tuntubi Matasa kamin ku bayar da Biliyin 75 na taimakonsu dan kada su sake fadawa wani Rumbun Ajiya>>Sanata Shehu Sani ga Gwamnati

Ku tuntubi Matasa kamin ku bayar da Biliyin 75 na taimakonsu dan kada su sake fadawa wani Rumbun Ajiya>>Sanata Shehu Sani ga Gwamnati

Siyasa
Sanata Shehu Sani ya baiwa gwamnatin tarayya Shawara kan yanda zata baiwa matasa tallafin Biliyan 75 na sana'o'i.   Gwamnati ta ware kudinne a karkashin ma'aikatar matasa da wasanni dan baiwa matasan jarin da zasu bunkasa kasuwancinsu wanda kuma tuni an fara Rijista. Sanata Sani yace Gwamnati ta tuntubi matasa kamin ta saki kudin dan kada su kare a wani rumbun Ajiya kuma.   To the FG;Seek the advice of the Youths before you disburse that N74 Billion,so that it doesn’t end up in ‘another warehouses’.
Gwamnati ta ware ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar Matasa

Gwamnati ta ware ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar Matasa

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta sanar da ware ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar matasa.   Hakan ya fitone daga zaman majalisar zartaswa na jiya bayan karbar rahoto daga kwamitin daka kafa dan samar da wannan rana a karkashin ministan matasa da wasanni, Sunday Dare. A kowace shekara za'a rika ware 1 ga wayan Nuwamba dan bikin wannan rana kamar yanda sanarwar ta tabbatar. Kuma za'a rika tabo batutuwan da suka shafi matasa.
An rabawa Gwamnoni da ‘yan Majalisa guraben ayyukan da gwamnatin tarayya zata ba matasa 774,000

An rabawa Gwamnoni da ‘yan Majalisa guraben ayyukan da gwamnatin tarayya zata ba matasa 774,000

Siyasa
Rahotanni daga Abuja na cewa an rabawa gwamnoni 'yan Majalisa da kungiyoyin addinai guraben daukar matasa 774,000 aiki da gwamnatin tarayya zata yi.   Bayan Gwamnoni da 'yan Majalisa akwai kuma Ministoci da Kwamishinoni da aka baiwa wannan guraben ayyuka. Hutudole ya ruwaito muku dambarwar da aka sha ta tsakanin Ministan gwadago da majalisa akan wannan daukar aiki. Saidai duk da kokarin dakatar da daukar aikin da majalisar ta yi, an ci gaba da yinsa inda yanzu haka a jihohi da dama ayyuka sun kankama. Hutudole ya ruwaito muku cewa, wannan aiki zai kasancene na watanni 3 inda za'a rika biyan matasan alawus din dubu 20 duk wata.   Gwamnati ta ware Biliyan 52 a kasafin kudin shekarar 2020 dan yin wannan aiki. Kamar yanda Hutudole ya samo muku daga TheNation. Wani ...
Ku nemi tallafin Biliyan 75 dana ware a baku dan sana’a>>Shugaba Buhari ga matasan Najeriya

Ku nemi tallafin Biliyan 75 dana ware a baku dan sana’a>>Shugaba Buhari ga matasan Najeriya

Siyasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bukaci matasan Najeriya da kada su yi kasa a gwiwa su nemi tallafin kudinnan da ya ware watau Biliyan 75 dan a basu su yi sana'a.   Shugaban ya bayyana hakane a yau a matsayin sakonsa na ranar matasa ta shafinshi na sada zumunta. Hutudole ya kawo muku cewa shugaba Buhari yace kwanannan suka kaddamar da shirin ware Biliyan 75 a matsayin wani yunkuri na samarwa matasa ayyukan yi.   Shugaban yace zai yi amfani da wannan rana ta matasa ya bukaci su nemi wannan tallafi dan damace a garesu. https://twitter.com/MBuhari/status/1293616737850621953?s=19
Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Biliyan 75 dan baiwa matasa tallafin sana’o’i

Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Biliyan 75 dan baiwa matasa tallafin sana’o’i

Siyasa
Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da Biliyan 75 dan baiwa matasa tallafin sana'o'in dogaro da kai.   Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare ya bayyana haka inda yace a karin farko a tarihin Najeriya gashi matasa sun samu abinda za'a iya kira da bankin matasa. Yace matasa daga shekarun 18 zuwa 35 ne zasu amfana da wannan tallafi inda yace ta yanar gizo za'a yi amfani dan karbar bayanan kasuwancin matasan, kuma wanda suka cancanta zasu samu wannan tallafi.   Yace majalisar Zartaswa ce ta amince da fitar da wannan kudi kuma za'a baiwa duk wanda suka cancanta ba tare da lura daga bangare ko kabilar da suka fito ba.