
Akwai matsaloli da yawa da ya kamata ace an magance ma ‘yan Najeriya su ba gyaran matatun mai ma>>Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki gwamnati kan ware dala biliyan ɗaya da rabi domin a gyara a matatan mai na Fatakwal.
A wasu sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da "rashin tattalin kalilan kuɗin da ake dasu" ana fama da dimbin matsalolin tattalin arziki.
Sannan ya ce har yanzu ana kan karbo bashi wajen aiwatar da manyan ayyuka a ƙasar.
"Basusukan da ake bin Najeriya ya ƙaru daga naira tirliyan 12 a 2015 zuwa naira triliyan 32.9 a 2021."
Atiku ya bada misali na taɓarɓarewar tattalin arziki wanda sanin kowa ne a ciki da wajen ƙasar. Ya ce rashin aikinyi ya karu da kashi 33 cikin 100 ga kuma hauhawan firashin kayayyakin masarufi.
Atiku ya ce akwai fannoni da dama da ke bukatar a mayarda hankali wajen farfado da tattali...